Ku daura laifin rashin tsaro a kan shugabannin tsaro - Gwamna Masari

Ku daura laifin rashin tsaro a kan shugabannin tsaro - Gwamna Masari

- Gwamna Aminu Masari ya daura laifin rashin tsaron da ya addabi jiharsa a kan shugabannin tsaron kasar nan

- Masari ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi duk abinda ya dace don tabbatar da tsaro a yankin

- Ya ce 'yan bindigar a yanzu basaja suke suna rayuwa da mutane

- Jihar Katsina na fama da hare-haren 'yan bindiga tare da wasu jihohin arewa maso yamma a kasar nan

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, a ranar Asabar ya daura laifin rashin tsaron da ya addabi jiharsa a kan shugabannin tsaron kasar nan.

Kamar yadda Masari ya ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi duk abinda ya dace don tabbatar da tsaro a yankin.

Ya yi wannan jawabin ne yayin mika tallafin N10 miliyan ga mata 1,000 da kuma N7 miliyan na tallafin karatu ga dalibai 701 a karamar hukumar Rimi ta jihar.

Ku daura laifin rashin tsaro a kan shugabannin tsaro - Gwamna Masari
Ku daura laifin rashin tsaro a kan shugabannin tsaro - Gwamna Masari Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Gwamnan ya ce ya kasa fahimtar abinda yasa shugabannin tsaron suka kasa taimakon yankin tunda su ma duk 'yan arewa ne.

Ya kara da cewa, 'yan bindigar a yanzu basaja suke suna rayuwa da mutane Channel TV ta ruwaito.

"Mun sansu da iyayensu," yace.

"Bayyana 'yan bindiga a karkara ba abu ne mai wahala ba, kun san aikinsu, gonarsu da kuma dabbobinsu.

"Idan kuwa ka ga ya siya babur na N200,000, toh tabbas ka san rayukan jama'a yake siyarwa."

Jihar Katsina wacce ita ce jihar shugaban kasa Muhammadu Buhari na fama da hare-haren 'yan bindiga tare da wasu jihohin arewa maso yamma a kasar nan.

A ranar 10 ga watan Augusta, 'yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Kurfi ta jihar tare da yin awon gaba da yarinya mai shekaru 13.

KU KARANTA KUMA: Bidiyo: Sojoji sun yi luguden wuta a sansanin 'yan ta'addan Ansaru a dajin Kuduru

A watan Yuni, matasa sun hau manyan titunan jihar inda suka dinga zanga-zanga a kan rashe-rashen rayuka da kadarorin da ake yi sakamakon harin 'yan bindiga.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabannin tsaron da su dage da aiki a yankin don bada kariya da ta dace.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel