Baga: Buratai ya kaddamar da bincike cikin zargin manyan Soji da yin noma da suna maimakon yaki

Baga: Buratai ya kaddamar da bincike cikin zargin manyan Soji da yin noma da suna maimakon yaki

Hukumar Sojin Najeriya karkashin Janar Tukur Yusuf Buratai ta kaddamar da bincike cikin zargin da ake yiwa manyan Sojin rundunar Operation Lafiya Dole a garin Baga, jihar Borno Arewa maso gabashin Najeriya.

An yi zargin manyan Soji da mayar da hankali wajen noma da suna a tafkin Chadi maimakon kawar yan Boko Haram dake jihar.

An fara zargin Sojojin ne bayan harin da aka kaiwa gwamnan jihar, Babangana Zulum a Baga, karamar hukumar Kukawa.

Yanzu, mataimakin kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Felix Omoigui, na jagorantar kwamitin binciken zargin kuma sun garzaya Baga don ganewa idanuwansu abinda ke faruwa.

Rundunar da ake zargi da wannan abu itace 130 battalion kuma gwamnan na kyautata zaton su suka kaiwa tawagar mototcinsa hari.

Kwamitin binciken ta yiwa kwamandan 130 battalion tambayoyi da kuma kwamandan rundunar CJTF.

Yayin amsa tambayoyi, kwamandan 130 battalion , Laftanar Kanal Umar AbdulMajid ya karyata wannan zargi da ake masa inda yace "babu gaskiya cikin lamarin, babu jami'in Soja ko mai farin hula dake noma ko kiwon kifi."

"Babu wani farin hula dake rayuwa tsakanin Monguno da Baga kuma babu motocin fararen hula dake shiga Baga."

A na shi bangaren, Manjo Janar Felix Omogui ya bayyana manema labarai cewa: "Babban Hafsan Soji ya samu labari kuma tun da mutum ne lamuntan abubuwan irin wannan, ya umurcemu mu zo mu gudanar da bincike kan gaskiyar lamarin."

"Yayin gudanar da binciken kuma kun shaida, zamu koma mu rubuta rahoton bincikenmu kuma zamu bayyanawa duniya."

Baga: Buratai ya kaddamar da bincike cikin zargin manyan Soji da yin noma da suna maimakon yaki
Baga: Buratai ya kaddamar da bincike cikin zargin manyan Soji da yin noma da suna maimakon yaki
Asali: UGC

Jiya mun kawo muku rahoton cewa majiya mai siqa cewa wasu manyan Sojoji sun yi watsi da aikinsu sun mayar da hankali wajen aikin noma da kiwon kifi a gonakin mutane.

Majiyar tace: "Babbar matsalar itace wasu manyan jami'an soji sun mayar da Baga wata cibiyar kasuwancinsu.

"Suna sana'ar sayar da kifi da tsuntsaye. A wannan sana'ar ne suke samun makudan kudaden da ake gani suna samu.

"Garin Baga na samar da kashi 45 na busasshen kifin da ake amfani da shi a Nigeria. Tana daya daga cikin garuruwa masu albarkar kasar noman tumatur da kayan lambu a kasar.

"Da yawa daga cikin wadannan jami'an sun saye tsuntsayen yanki baki daya.

"Daura da barikin soji na Baga a yanzu ya zama wata babbar gona, mallakin wani babban jami'in soji."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel