Batanci ga Annabi a Kano: Ku daina saka baki cikin lamuran Musulunci - Jikan Shagari ya gargadi Kirista

Batanci ga Annabi a Kano: Ku daina saka baki cikin lamuran Musulunci - Jikan Shagari ya gargadi Kirista

Bello Shagari, jikan tsohon shugaban kasan Najeriya, Marigayi Alhaji Shehu Shagari, ya yi kira ga mabiya addinin Kirista su daina saka baki cikin lamuran addinin Musulunci.

Shagari ya bayyana hakan ne yayinda yake tsokaci kan shari'ar babban kotun shari'a dake jihar Kano da ta yanke hukuncin kisa kan wani mawakin da yayi kalaman batanci kan fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu.

Bello Shagari yace: "Musulami su mayar da hankali kan Musuluncinsu, Kirista su mayar da hankali kan kiristancinsu kuma kafirai su mayar da hankali kan kafircinsu."

"Kowa ya mayar da hankali kan abinda yayi imani. Kada addinin wani ya dame ka, kuma kada wanda yayi kutse cikin addinin wani."

"Rashin adalci daya kawai nike da nike gani a hukuncin Shari'a a Najeriya shine kan talaka kawai take karewa ba, sai dai idan ba haddi bane,"

Matasa a kafafen ra'ayi da sada zumunta sunyi masa ca kan wannan jawabin da yayi.

Batanci ga Annabi a Kano: Ku daina saka baki cikin lamuran Musulunci - Jikan Shagari ya gargadi Kirista
Batanci ga Annabi a Kano: Ku daina saka baki cikin lamuran Musulunci - Jikan Shagari ya gargadi Kirista
Asali: Facebook

A bangare guda, Kungiyar SERAP ta yi tir da hukuncin da wani Alkalin babban kotun shari’a ya yanke na kisan kai a kan Yahaya Sharif-Aminu wanda ya zagi Manzon Allah a Kano.

A farkon makon nan ne Alkali mai shari’a Aliyu Kani ya samu yaro mai shekara 22 da laifin yin batanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.

Kungiyar ta SERAP ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi fatali da hukuncin da aka yi wa wannan matashi, ta ce Alkalin kotun shari’ar ya yi wa dokar kasa karon-tsaye.

A cewar SERAP, an tauyewa wannan Mawaki watau Yahaya Sharif-Aminu hakkinsa na magana a matsayinsa na ‘dan kasa da wannan hukuci da kotun shari’a ta yanke.

A dalilin wannan ne kungiyar ta fito ta na neman gwamnati ta sa baki, a saki Sharif-Aminu. SERAP ta bayyana wannan ne a shafinta na Twitter a ranar 11 ga wata Agusta, 2020.

Wannan kungiya ta ce hukuncin ya nuna yadda ake azabtar da talaka a Najeriya da rigar dokokin batanci. SERAP ta ce dokar ta na aiki ne kurum a kan talaka maras gata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel