NDDC: Dokokin shari’a da Injila ne za su yi maganin rashin gaskiya – inji Adeyami

NDDC: Dokokin shari’a da Injila ne za su yi maganin rashin gaskiya – inji Adeyami

Sanata mai wakiltar yammacin jihar Kogi, Smart Adeyemi, ya yi kira da a samu tsauraran dokoki domin yaki da rashin gaskiya a Najeriya.

Yayin da ake tattaunawa game da zargin badakalar da ake tafkawa a hukumar NDDC, Sanata Smart Adeyemi ya bada shawarar a canza salon dokokin kasa.

Sanatan ya yi kira ga majalisar dattawa ta dauko dokokin shari’ar addinin Musulunci da dokokin da su ka zo cikin Injila domin a magance satar dukiyar gwamnati.

Adeyemi, a wani bidiyonsa da ya shiga hannun Legit.ng Hausa, ya yi dogon jawabi a fusace, ya na Allah-wadai da yadda jami’an gwamnati su ke cin amanar kasa.

“Shugaban (majalisa), a Injila akwai dokar Annabi Musa, wanda a Kur’ani ake kira Shari’a. Irin barnar da ake yi a kasar nan ya fi karfin dokokin da mu ke da su.” Inji Smart Adeyemi.

Ya ce har yau ana fama da barna. “Mu na da dokokin majalisa 14 da su ke yaki da rashin gaskiya, gwamnatin nan ta yi amfani da taken yaki da barna ne domin hawa kan mulki.”

KU KARANTA: Buhari ya ba tsofaffin 'Yan majalisa mukami a Gwamnatin Tarayya

NDDC: Dokokin shari’a da Injila ne za su yi maganin rashin gaskiya – inji Adeyami
Sanata Smart Adeyami Hoto: Senate
Asali: Facebook

“Mecece mafita, shugaban (majalisa), dole mu kawo dokokin Shari’a da na Injila, datse hannu, da daurin rai da rai. Wannan shi ne abin yi wajen yaki da sata a Najeriya.”

Sanata Adeyemi ya kara da jan kunne cewa: “Mu na da zugar matasa da ba su da aikin yi a yau, mu na cikin hadari, iyalinmu su na cikin hadari.”

“An ba wasu damar kula da wani yanki amma dubi abin da su ke yi! Naira biliyan 3.2 sun tafi kan kayan asibiti. Ba za ka taba iya yi wa jama’a bayanin wannan ba.”

‘Dan majalisar ya ce ya ji dadi da ya ga mutanen Neja-Delta ne ake zargi da badakala a NDDC, don haka ba za a samu damar zargin ‘yan wasu yanki da yi masu ba-ba-ke-re ba.

“Kun kashe Naira biliyan 81 a cikin watanni shida. Kuma babu abin da za a zo a gani.”

Yayin da ya ke bayani, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya gargadi Adeyemi da ya tsaya a hurumin da doka ta ba shi, ka da ya zarce makadi da rawa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel