Ruwan sama ke kawo cikas wurin yaƙi da ƴan bindiga, inji Masari

Ruwan sama ke kawo cikas wurin yaƙi da ƴan bindiga, inji Masari

Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, a ranar Laraba ya ce ruwan sama da ake yi kamar da bakin kwarya na daya daga cikin kallubalen da hukumomin tsaron da ke yaki da 'yan bindiga a yankin arewa ke fuskanta.

Masari ya kuma bayyana fargabar cewa rashin zaman lafiyan da ake fama da ita a sassan kasar nan na iya barazana ga samar da abinci a kasar.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin zantawarsa da manema labarai a gidan gwamnati bayan taron da ya yi da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa ta Aso Rock Villa a Abuja.

Ruwan sama ke kawo cikas wurin yaƙi da ƴan bindiga, inji Masari
Aminu Masari. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

Masari ya ce jamian tsaron suna fuskantar kallubale wurin zirga zirga na motocin yaki na sojoji a lokacin damina saboda laushin kasar da ke dajin da yan bindigan suke fakewa.

DUBA WANNAN: An yi sulhu tsakanin Bafarawa da Wamakko

Amma duk da hakan ya bayyana gamsuwarsa cewa za a magance kallubalen kuma za a samu nasara a kansu.

Gwamnan ya ce, "Akwai daji masu girma da hanyoyi masu wahalar bi a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Tsakiya inda yan bindigan ke buya.

Yanzu lokacin damina mu ke, akwai wahalar tafiya da manyan motocin yaki na sojoji domin kasar laushi gare ta kuma ruwan sama ya yi yawa. Amma dai za a cimma buri. Babu abinda ba zai yi wu ba idan har akwai niyya kuma an dage."

Masari ya ce a halin yanzu akwai sojoji kimanin 2,000 a Katsina inda za su yi taron su na shekara wadda hakan alama ce da ke nuna wa yan bindigan cewa sojojin sun shirya tsaf don yin maganinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel