Idan har da gaske Oshiomhole ya yi boko, ya fito da satifiket din firamarensa – PDP

Idan har da gaske Oshiomhole ya yi boko, ya fito da satifiket din firamarensa – PDP

- PDP ta sake dura kan tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole

- Jam’iyyar PDP ta reshen jihar Edo ta kalubalanci Oshiomhole ya fito da satifiket dinsa

- PDP ta na zargin cewa Oshiomhole ba zai iya kawo ko takardar kammala firamare ba

Jam’iyyar PDP ta jihar Edo ta bukaci tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya fito da takardun shaidan da ke nuna lallai ya kammala makarantar boko.

PDP kalubalanci Kwamred Adams Oshiomhole ya gabatar da satifiket dinsa na kammala aji shida na firamare domin Duniya ta gamsu cewa ya taba zuwa makaranta.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa babbar jam’iyyar PDP adawar ta yi wannan kira ne a cikin farkon makon nan ta bakin babban jigonta a jihar Edo, Cif Dan Orbih.

Da ya ke magana da wasu ‘ya ‘yan jam’iyya na mazabar Ososo da Dangbala na karamar hukumar Akoko-Edo, Dan Orbih ya ce Oshiomhole bai shiga aji ba.

KU KARANTA: Abin da ya sa aka sauke ni daga Shugaban APC - Oshiomhole

Idan har da gaske Oshiomhole ya yi boko, ya fito da satifiket din firamarensa – PDP
Cif Dan Orbih
Asali: Twitter

Bayan zargin rashin zuwa makarantar boko, jagoran neman tazarcen Obaseki, Dan Orbih, ya ce gwamnatin da ke ci yanzu ta yi abin da ya zarce duk aikin Oshiomhole.

“Sun ce gwamna Godwin Obaseki wanda ya yi karatu a jami’ar Ibadan ya na da satifiket. Na fito da babbar murya, ina kalubalantar Adams Oshiomhole ya nuna mana satifiket dinsa na firamare.”

Orbih ya kara da cewa: “Ya kyale mutanen Edo su zabi wanda su ke so ya mulke su. A shekaru hudu, Godwin Obaseki ya yi fiye da abin da Oshiomhole ya yi a shekara takwas.”

Rahoton ya nuna cewa Godwin Obaseki ya yi magana a wajen wannan taro, inda ya bada sanarwar karasa aikin Ososo zuwa Okpella da Oshiomhole ya yi watsi da shi.

Kawo yanzu dai ba mu samu labarin cewa Oshiomhole ya maidawa Dan Orbih martani ba. Kwanaki hudu da yin maganar, tsohon gwamnan bai fito da takardunsa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel