Ya zarce 4: Sarkin Oyo mai shekaru 81 tare da 7 cikin matansa a hoton Sallah

Ya zarce 4: Sarkin Oyo mai shekaru 81 tare da 7 cikin matansa a hoton Sallah

- Sarkin Oyo, Oba Lamidi Olyiwola Adeyemi III, tare da iyalansa sun yi murnan babban Sallan bana

- Yayin murnan, Sarkin ya dauki hoto tare da amarensa bakwai

- Matan sun sanya kaya iri daya yayinda suka zagayeshi a cikin fadarsa

Yayinda al'ummar Musulmai suke murnan babban Sallah ranar Juma'a, 31 ga Yuli, babban Sarki a kasar Yarbawa, ya yi murnar da iyalin a fadar masarautar dake jihar Oyo.

Yayin murnar, sarkin ya dauki hotuna da amarensa bakwai.

Masu sharhi kan al'aumuran yau da kullum sun yi tsokaci kan kasancewar Sarkin ya auri mata fiye da hudu duk da kasancewarsa Musulmi.

A hoton, an ga kananan matansa bakwai, banda manyan da basu shiga hoton ba.

Ya zarce 4: Sarkin Oyo mai shekaru 81 tare da 7 cikin matansa a hoton Sallah
Ya zarce 4: Sarkin Oyo mai shekaru 81 tare da 7 cikin matansa a hoton Sallah
Asali: Instagram

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng