Buhari ya jinjinawa kwamitin rikon kwarya na APC

Buhari ya jinjinawa kwamitin rikon kwarya na APC

- Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjinawa kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni

- Shugaba Buhari ya kuma jinjinawa kungiyar gwamnonin APC, wacce Atiku Bagudu, gwamnan jihar Kebbi ke jagoranta kan yadda suke kokari da jam'iyyar

- Hakazalika Gwamna Atiku Bagudu ya mika godiya ga shugaban kasar da ya dauki matakin da ya dace wurin shawo kan matsalar jam'iyyar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa Gwamna Mai Mala Buni a bisa jagorancin da yake wa kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC.

Shugaban kasar ya jinjinawa kungiyar gwamnonin APC, wacce Atiku Bagudu, gwamnan jihar Kebbi ke jagoranta kan yadda suke kokari a zaben jihohin Edo da Ondo ke gabatowa.

A wata takarda da kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya fitar, ya bayyana cewa Buhari ya jinjinawa Buni a kan kokarin da ya yi wurin kawo zaman lafiya a jam'iyyar.

Bayan rushe kwamitin gudanarwa na APC ta kasa a watan Yuni, an nada gwamnan jihar Yobe, da wasu a matsayin 'yan kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar.

Buhari ya jinjinawa kwamitin rikon kwarya na APC
Buhari ya jinjinawa kwamitin rikon kwarya na APC Hoto: Bahir Ahmad
Asali: Twitter

A ranar Talata, 28 ga watan Yuli, yayin taron da Buhari yayi ta yanar gizo da gwamnonin jam'iyyar mai mulki, ya ce yana matukar farin ciki da aikin kwamitin rikon kwaryar.

Kamar yadda yace: "ina farin ciki da shugaban kwamitin rikon kwarya da kuma ayyukansa. Yana yin dukkan kokarin da ya dace wurin ganin ya gyara tare da karfafa jam'iyyar. Ina farin ciki da kokarinsa."

Shugaba Buhari ya jinjinawa kokarin gwamnonin APC bayan nasarar da aka samu wurin zaben fidda gwani na jihohin Edo da Ondo, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Idan kun isa ku ce kule ku gani a kan yaki da rashawa - Buhari ya yi wa PDP martani

Ya kara da cewa, "ina farin cikin ganin cewa sun san hakkin da ke kansu a matsayin gwamnoni tare da gano abubuwan da ya kamata su bai wa fifiko."

A yayin jawabi a madadin takwarorinsa, Bagudu ya mika godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki matakin da ya dace wurin shawo kan matsalar jam'iyyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel