Jihar Katsina da Bayelsa su na cikin Jihohin da su ka fi dogara da asusun FAAC

Jihar Katsina da Bayelsa su na cikin Jihohin da su ka fi dogara da asusun FAAC

Alkaluman ASCI na halin da jihohin su ke ciki da aka fitar a ranar Lahadi, 26 ga watan Yuli ya nuna cewa jihohi shida a Najeriya kadai su ke tsaye a kan kafafunsu a halin yanzu.

Economic Confidential ta ce alkaluma sun tabbatar Katsina ta na cikin jihohi marasa arziki a kasar. Sauran jihohin da ke cikin wannan sahu su ne: Kebbi, Borno, Bayelsa da jihar Taraba.

Abin da wannan ya ke nufi shi ne mafi yawan jihohi ba su samun kudi masu yawa ta haraji watau IGR. Ana samun kudin shiga ne daga albashin ma’aikata, harajin hanya da sauransu.

A 2019, abin da jihohi su ka iya tatsowa da kansu a matsayin kudin shiga ya kai Naira tiriliyan 1.3. Jihar shugaban kasa watau Katsina, ta na cikin masu karancin kudin shiga.

Rahoton ya nuna Katsina ta iya tatso IGR na Naira biliyan 8 ne kacal a shekarar bara, amma ta samu kudi har Naira biliyan 136 daga asusun FAAC na gwamnatin tarayya.

Jihar Legas kuwa ta samu kusan Naira biliyan 400 a matsayin kudin shiga, IGR din jihar ya haura abin da jihohin kasar 20 su ka taru su ka tatsa a cikin shekarar 2019.

KU KARANTA: s

Jihar Katsina da Bayelsa su na cikin Jihohin da su ka fi dogara da asusun FAAC
Shugaban kasa Buhari Hoto: State House
Asali: UGC

Ogun ce ta ke bin bayan Legas a sahun IGR da Naira biliyan 70. Abin da gwamnonin Legas da Ogun su ka karba daga hannun gwamnatin tarayya a bara bai wuce Biliyan 360 ba.

Ribas ta samu Naira biliyan 219 daga asusun FAAC, amma gwamnatin jihar ta karbi harajin Naira biliyan 140 a hannun talakawa. Wata jihar da ke wannan sahu ita ce Kwara mai IGR na biliyan 30.

Kaduna ta karshe a cikin jihohin da su ke da kafi, ta samu kudin-shiga na Naira biliyan 44. Abin da jihar ta karba daga asusun gwamnatin tarayya ya kai Naira biliyan 120.

Jihar Enugu, Ondo, Anambra da Kuros-Riba ne su ka cike jerin sahun goman farko na jihohin da su ke da arzikin IGR a Najeriya. Daga cikinsu biyu ne kurum daga yankin Arewa.

Birnin tarayya ya samu kason Naira biliyan 30 daga asusun tarayya, a IGR kuwa, ministan Abuja ya samu abin da ya haura Naira biliyan 70 a matsayin kudin shiga.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng