Sama da mutane 20 sun kone kurmus sakamakon fashewar tankar mai a Delta

Sama da mutane 20 sun kone kurmus sakamakon fashewar tankar mai a Delta

Akalla mutane 20 ake hasashen sun rasa rayukansu bayan da wata tanka makare da man fetur ta kama da wuta a sha-tale-talen Koko, kan titin Benin zuwa Saepele, a karamar hukumar Ethiope ta Yamma, jihar Delta.

Lamarin, a cewar wata majiya, ya faru ne da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Laraba.

Wakilin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa tankar ta fashe tare da kamawa da wuta bayan da ta fada cikin wani rami kan sha-tale-talen Koko da Ologbo, babban titin Benin zuwa Sapele, karamar hukumar Ethiope ta Yamma, jihar Delta.

Ababen hawa da dama da ke tafiya akan hanyar lamarin ya rutsa dasu inda da yawansu suka kone, kamar yadda wani fasinja da ya sha dakyar ya shaidawa manema labarai.

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda hatsarin ya rutsa dasu sun kone kurmus ta yadda ba za a iya gane su, yayin da motoci sama da 10 suka kama da wuta.

Wata da hatsarin ya faru a kan idonta ta ce tankar ta tunkari Sapele ne daga Benin, ita kuma lokacin tana cikin mota kirar Nissan Quest tare da wasu fasinjoji.

KARANTA WANNAN: Guguwar Buhari ba zata yima aiki a 2023 ba, APC ta gargadi mambobinta

Sama da mutane 20 sun mutu sakamakon fashewar tankar mai a Delta
Sama da mutane 20 sun mutu sakamakon fashewar tankar mai a Delta
Asali: UGC

"Tankar na dauke da man fetur, a kokarinta na kaucewa wani rami ne ta jirkice, inda nan take ta kama da wuta, a tsakanin sha-tale-talen Koko da Ologbo.

"Hatsarin ya munana kwarai, ya rutsa da mutane da dama, motoci da dama sun kama da wuta.

"A karshe, motoci masu dauke da fasinjoji 10 sun kone kurmus inda sama da gawarwaki 20 aka ciro daga cikin motocin.

"Mu munci sa'a lokacin da muke a wajen har 'yan kwana kwana sun iso kuma suka fara kokarin kashe wutar.

"Hatsarin ya rutsa da mutane da dama a cikin motonsu, saboda cunkuson wajen yasa ya zamo wahala wajen cetonsu, gashi wutar na ci sosai," a cewarsa.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, da misalin karfe 3:00 na rana, jami'an hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC, na ci gaba da ceto mutane daga inda hatsarin ya auku.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel