Matashi ya cire kan abokin aikinsa bayan ya ga N13m a asusun bankinsa

Matashi ya cire kan abokin aikinsa bayan ya ga N13m a asusun bankinsa

Wani matashi mai shekaru 29 ta sheka lahira bayan sanar da abokinsa makuden kudin da ke asusun bankinsa, wanda yayansa da ke kasar Afrika ta Kudu ya turo masa don kammala ginin gidansa a Najeriya.

Moses ya halaka abokinsa Abuchi Wisdom Nwachukwu har lahira, bayan sanar da shi da yayi akwai Naira miliyan 13 a asusun bankinsa.

Nwachukwu dan asalin karamar hukumar Isiala-Mbano ne da ke jihar Imo. Ana zargin an kashesa ne a ranar 7 ga watan Janairun 2020 a yayin da yake aikin dare a wani gidan ruwa da ke Auchi a jihar Edo. Daga nan wanda ake zargin ya dauke waya tare da ATM na mamacin.

Moses ya cire kan abokinsa Nwachukwu daga gangar jikinsa ta yadda ba za a ganeshi ba, kuma ya yasar da gangar jikin da babu kai a wani daji da ke kusa da kamfanin.

Bayan yasar da gawar Nwachukwu, Moses ya dauke wayarsa tare da ATM din shi, wanda ya kai wa wasu masu damfarar yanar gizo inda suka kwashe N2.2 miliyan daga asusun bankinsa.

Bayan nan, Moses ya garzaya wurin cire kudi da yawa da ke garin inda ya dinga zare kudin.

Jami'an tsaro sun shiga wani hali bayan da suka samu gangar jikin Nwachukwu babu kai, hakan yasa suka kasa gane mamacin. A can jihar Imo kuwa, iyayen Nwachukwu sun shiga tashin hankali sakamakon batansa da kuma rashin samunsa a waya.

Yayansa da ke kasar Afrika ta Kudu ya mika korafinsa ga sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Adamu Mohammed, bayan watannin da ya kwashe bai ji kaninsa ba.

Jami'an runduna ta musamman karkashin shugabancin Abba Kyari, mataimakin kwamishinan 'yan sanda, suka bazama nemansa inda suka bankado gaskiyar al'amarin.

Bayan makonni kadan da fara bincikensu ne suka fara gani inda ake cire kudi da katin bankin Nwachukwu a Benin, Ore da Auchi a jihar Edo.

Daga bisani sun damke wanda ke rike da katin a wani otal da ke Auchi.

Bayan tuhumarsa, Moses ya amsa laifin kashe Nwachukwu. Ya jagoranci rundunar ta musamman ga 'yan damfarar yanar gizon tare da dan kasuwan da suka taimaka masa wurin cire N6 miliyan daga asusun bankin.

Moses ya bayyana yadda ya rasa kwanciyar hankali tun bayan da ya kashe abokinsa.

Matashi ya cire kan abokin aikinsa bayan ya ga N13m a asusun bankinsa
Matashi ya cire kan abokin aikinsa bayan ya ga N13m a asusun bankinsa. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: 'Yan sanda sun zagaye gidan tsohuwar MD ta NDDC

Ya ce: "Ina aiki a wani gidan ruwa da ke yankin Abely a Auchi kuma an kwashe shekaru hudu ina aikin.

"Lokacin da Nwachukwu ya samu aikin, ni na koya masa yadda ake komai kuma muka zama abokai makusanta.

"A lokacin da muke aiki, Nwachukwu ya sanar da ni cewa yana da dan uwa a kasar Afrika ta Kudu da kuma yadda yake turo masa kudi yana gina masa gida.

"Ya nuna min shigowar kudi har N13 miliyan wanda yace don haka zai tafi kauyensu don a ci gaba da aikin. A take kishi da hassada suka mamaye zuciyata kuma an yanke hukuncin sace kudin.

"Saboda kusancin da muke da shi, na karba lambobin bude wayarsa inda a nan na gano na katin bankinsa.

"Bayan kwanaki kadan, na ja shi wajen kamfani da dare inda na soka masa wuka tare da kasheshi. Na ja gawarsa cikin daji kuma saboda kada a gane shi da wuri, sai na cire kanshi na birne.

"Daga nan na kai wa masu damfarar yanar gizo katin bankinsa. Mun cire N2.2 miliyan. Mun yi fada da su saboda suna son cuta ta. Na kashe shi a ranar 8 ga watan Janairun 2020 kuma na je Ore da Benin.

"Na zauna a otal daban-daban tare da diban karuwai kala-kala. Amma kuma hankalina ya kasa kwanciya saboda fatalwa yake min.

"Idan na zo bacci, fatalwarshi na bayyana kuma ina ganinsa yana kuka. Matan da na kwaso suna guduwa su barni saboda zargin zan yi tsafi da su."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel