Binciken NDDC: ‘Yan Najeriya za su cigaba da ji daga gare ni – inji Joy Nunieh
A ranar Alhamis, 16 ga watan Yuli, 2020, shugabar hukumar NDDC da aka sallama daga aiki, ta yi alkawarin cewa ‘yan Najeriya za su ji labarin ta’adin da aka yi a gwamnati.
Dr. Joy Nunieh ta bayyana wannan ne yayin da ta ke tsakiyar rigima da Ministar harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio da majalisar tarayya a kan badakalar NDDC.
Joy Nunieh ta yi jawabi ne a gidan gwamnatin jihar Ribas bayan gwamna Nyesom Wike ya cece ta daga hannun ‘yan sanda. Ana zargin an yi yunkurin hana Nunieh hallara ne gaban majalisa.
Jaridar Vanguard ta ce dakarun Mopol sun dura gidan Joy Nunieh da ke layin Herbert Macaulay a unguwar GRA, Fatakwal, a jihar ne da karfe 4:00 domin hana ta tafiya zuwa Abuja.
“Ina jin na samu tsaro a gidan gwamnati. Akpabio ba zai iya kashe ni ba. Daga garin Uyo na ke. Ina tunanin ya na kokarin hana ni zuwa gaban majalisa ne.”
KU KARANTA: Tsohuwar Shugabar NDDC ta bada labarin yadda aka dura gidanta
Ta kara da cewa: “Yayi nasara amma ina tunanin ‘yan majalisar wakilan tarayya za su sake ba ni dama, kuma ‘yan Najeriya za su ji fiye da haka.”
“Na daina magana, amma abin da na ke so shi ne in gabata gaban majalisa. Da haka ‘Yan Najeriya za su ji bayanai sosai. Masu iya magana su na cewa wadanda su ka yi tsit, za su zauna karkashin sakarkaru.”
“Ministan (Akpabio) ya na tunanin zai iya yi mani barazana da ‘yan sanda, amma ba za a ba ni tsoro ba. Yana tsoron tonon asirin da na yi, da na ce babu binciken da ake yi a NDDC.”
“Jiya, BPP sun bayyana gaban kwamiti kuma sun bayyana cewa Akpabio ya tursasa su wajen bada satifiket bayan ya fada masu an amince da kasafin kudin 2020.”
Jami’ar gwamnatin da aka dakatar ta ce ko ba-jima ko ba-dade, za ta zauna gaban ‘yan majalisa, ta bayyana masu abin da ta san ya faru a ma’aikatar da ke kula da Neja-Delta.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng