Tsohon Gwamna Fayose ya ba Falana shawarar ya tafi kotu kan batun Magu

Tsohon Gwamna Fayose ya ba Falana shawarar ya tafi kotu kan batun Magu

- Ana jita-jitar cewa Ibrahim Magu ya ba Femi Falana wasu makudan kudi

- Lauyan ya karyata wannan zargi, ya yi barazanar karar masu masa kazafi

- Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose ya sa baki a cikin wannan lamari

Ayodele Fayose, wanda ya yi mulki a jihar Ekiti a baya, ya yi magana game da rade-radin alakar tsohon shugaban EFCC, Ibrahim Magu da Femi Falana.

Ana zargin cewa shararren lauyan ya na da hannu a wasu badakalar da ake zargin shugaban na hukumar EFCC da aka dakatar da aikatawa.

Mista Ayodele Fayose ya yi amfani da shafinsa na Twitter a ranar Laraba, 15 ga watan Yuli, 2020, ya na kira ga Femi Falana ya tafi gaban kotu domin ya wanke kansa.

Fayose ya fadawa lauyan da ya yi fice wajen kare hakkin Bil Adama da ya daina yi wa jama’a barazanar kawai, idan har ya na tunanin cewa ya na da gaskiya.

Hakan na zuwa ne bayan lauyan Femi Falana SAN ya fito ya karyata zargin cewa mai gidansa ya karbi Naira miliyan 28 daga hannun Ibrahim Magu.

KU KARANTA: Buhari: Abin da ya sa mu ka turke Magu

Tsohon Gwamna Fayose ya ba Falana shawarar ya tafi kotu kan batun Magu
Femi Falana SAN
Asali: UGC

Lauyan da ke kare Falana watau Olumide-Fusika, ya ce babu lokacin da mai gidansa ya amshi kudi daga hannun Magu wanda ake tuhuma. Ya ce Duniya ta shaida nagartar Falana.

Mista Fayose ya ce idan har Lauyan bai da wani abin da ya ke tsoron a bankado, ya je kotu inda za a gane mai gaskiya.

"Idan har babu abin da zai boye, meyasa Femi Falana ya ke barazana, maimakon ya tafi kotu cikin sauki? Shin zargin wannan badakala ta Magu ba dama ba ce da zai je kotu ya wanke kansa?"

"Ina ganin ya kamata ire-irensa su daina yi kamar su din wasu waliyyai ne wanda su ka gagari a taba su."

Tsohon gwamnan na Ekiti ya ce: ""Shawara ta ga Falana ya daina barazanar banza, ya tafi gaban kuliya."

Kwanakin baya Fayose wanda ya yi gwamna sau biyu ya bada shawarar a tsare Magu, sannan ya zargi EFCC a karkashinsa da saidawa abokansa kadarorin da aka karbe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng