Sojoji 37 aka kashe a harin hanyar Maiduguri zuwa Damboa - Majiyoyi

Sojoji 37 aka kashe a harin hanyar Maiduguri zuwa Damboa - Majiyoyi

Akalla Dakarun Sojojin Najeriya da aka yiwa horon na musamman guda 37 sun rasa rayukansu yayinda saura da dama suka jikkata a harin kwantan bauna da yan Boko Haram suka kaiwa Sojoji.

An tattaro cewa harin ya auku ne a hanyar Maiduguri zuwa Damboa, ana saura kimanin kilomita 30 da garin Damboa ranar Talata, 7 ga watan Yuli, 2020.

Wannan rahoto da Premium Times ya saba jawabin da hukumar Sojin Najeriya ta saki na adadin sojin da suka mutu.

Jagoran sashen yada labaran hedkwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche ya ce Sojoji biyu kadai aka kashe.

Ya sanar da cewa, a wani kicibus da ta yi da mayakan Boko Haram a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri, 'yan ta'adda 17 sun bakunci lahira.

Amma a cewar masu idanun shaida da ke da masaniya kan lamarin, sun ce hukumar Soji na karyar ainihin abinda ya faru.

Majiyoyin wanda suka hada da Sojojin dake bakin fama sun tuhumci shugabanninsu da kokarin boye ainihin abinda ya faru.

KU KARANTA: An kirkiri sabon na'urar gwajin cutar Korona a Najeriya

Sojoji 37 aka kashe a harin hanyar Maiduguri zuwa Damboa - Majiyoyi
Sojoji 37 aka kashe a harin hanyar Maiduguri zuwa Damboa - Majiyoyi
Asali: Twitter

Daga daga cikin majiyoyin yace "Harin ya auku misalin karfe 7 na yammacin ranar Talata yayinda dakarun sojin 25 task force brigade, Sector 2, da 402/Special Task Force suka tashi daga Hedkwata domin sintiri tare a hanyar Damboa-Maiduguri."

"Kawai sai sukayi kicibis da wasu yan Boko Haram da ba'a son adadinsu ba suka far ma sojojin tsakanin kauyukan Limanti da Bulabulin, babu nisa da Damboa."

"Da farko gawawwakin Sojoji 27 akakirga kafin aka gano wasu gawawwakin da kai adadin 37,"

Majiyar ta kara da cewa yan ta'addan sun yi awon gaba da motocin yakin Sojojin Najeriya hudu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel