Fadar Shugaban kasa ta sa Hukumar EFCC da Mutanen Najeriya sun shiga garari

Fadar Shugaban kasa ta sa Hukumar EFCC da Mutanen Najeriya sun shiga garari

- Mutane su na cikin duhu a game da halin da ake ciki yanzu a hukumar EFCC

- Haka zalika jami’an hukumar kasar ba su san halin da su ke ciki ba har yau

- Masana sun ce akwai bukatar gwamnati ta fito ta rika yi wa 'Yan kasa bayani

Kwanaki hudu da cafke Ibrahim Magu, har yanzu fadar shugaban kasar Najeriya ba ta iya fitowa ta yi wa jama’a jawabi ba. Jaridar Daily Trust ta rahoto wannan.

Har zuwa yanzu safiyar ranar Alhamis, gwamnatin Najeriya ba ta bayyanawa ‘yan kasa ainihin abin da ke faruwa game da binciken da ake yi a kan mukaddashin shugaban EFCC ba.

Bayan haka kuma gwamnatin tarayya ba ta fitar da wani jawabi a fili ba a kan maganar dakatar da Ibrahim Magu da aka yi daga kujerar da ya ke kai na kusan tsawon shekaru biyar.

A hukumar kasar, an shiga cikin hargitsi a dalilin rasa gane wanda zai zama sabon shugaba na rikon kwarya har zuwa lokacin da za a kammala binciken da ake yi a fadar shugaban kasa.

KU KARANTA: Magu bai taba ba Osinbajo Biliyoyin da ake fada ba

Fadar Shugaban kasa ta sa Hukumar EFCC da Mutanen Najeriya sun shiga garari
Shugaban Hukumar EFCC Hoto: EFCC
Asali: UGC

Sunaye na yawo na wadanda ake rade-radin za su jagoranci ragamar hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki barazana, amma babu wani jawabi daga bakin kakakin hukumar.

Lauyoyi da kungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu rajin yaki da sata a Najeriya sun dura kan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na yin abubuwa a asirce.

Tun daga ranar 6 ga watan Yuli, 2020, da aka fara samun labarin cewa an cafke Ibrahim Magu, fadar shugaban kasa ba ta yi magana ba, ta bar ‘yan kasa da tunani da hasashensu.

Garba Shehu, wanda ke magana da yawun bakin shugaban kasa ya musanya cewa an kama Magu, ya ce an gayyace shugaban EFCC ne gaban wani kwamiti domin yi masa tambayoyi.

Ministan shari’a, Abubakar Malami ta bakin hadiminsa, ya nuna bai da labarin abin da ke faruwa. Kwanaki Ministan ya rubutawa shugaban kasa takarda ya na tuhumar shugaban na EFCC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng