Mai Mala Buni ya bayyana dalilin sauya shekar mataimakin gwamnan Ondo da SSG
- An bayyana dalilin da ya sa wasu jiga-jigan a Ondo APC suka bar jam’iyyar yayinda ake shirin zaben gwamna a jihar
- Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar, Gwamna Mai Mala Bunin a Yobe ya yi zargin cewa manyan ‘ya’yan jam’iyyar sun bar APC ne saboda son zuciyarsu
- Buni na hannunka mai sanda ne ga mataimakin gwamnan jihar, Agboola Ajayi da sakataren gwamnatin jihar, Ifedayo Adegunde
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, kuma Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC ya bayyana dalilin da yasa wasu jiga-jigan jam’iyyar a Ondo suka barta.
Buni na hannunka mai sanda ne ga sauya shekar mataimakin gwamnan jihar, Agboola Ajayi da babban sakataren gwamnatin jihar, Ifedayo Adegunde.
A lokacin rantsar da kwamitin tantancewa da suararon korafi na jam’iyyar a zaben fidda gwani a jihar, Buni ya yi zargin cewa son zuciya ne ya sa Ajayi da Adegunde barin APC.
Ya kara da cewar sun bar jam’iyyar ne saboda kudirinsu na tsayawa takara.
Gwamnan na Yobe ya ce: “Duk mu sani cewa, kudiri na daban da son zuciya ne kan sa mutane aiki ba tare da tunani ba.”
Ya kuma ba dukkanin yan takarar gwamna a zaben fidda gwani na jam’iyyar a jihar Ondo tabbacin cewa za a basu filin fafatawa daidai da tsarin jam’iyyar na adalci da gaskiya.
“Muna iya baku tabbacin cewa yan takara, wadanda suka nuna ra’ayin neman rike tutar jam’iyyarmu a zaben Ondo, za su samu adalci iri guda, kuma za a yi zabe cikin gaskiya da amana daidai da tsarin fitar da gwaji,” in ji jam’iyyar.
Ya bukaci kwamitin da su zama adalai, inda ya ce an zabe su ne domin an ga sun kasance mutane masu gaskiya da cancanta wajen tantance dukkanin yan takarar.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ngige ya bayar da hakuri a kan furucin Keyamo game da ayyuka 774,000
Ya kuma gargadi mambobin kwamitin cewa ayyukansu wajen sauke nauyin da aka daura masu na iya gyarawa da kuma bata martabar jam’iyyar.
Ya shawarce su da su yi iya bakin kokarinsu wajen kammanta gaskiya da adalci.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng