Fetur: Sani ya yi tir da hukumar PPPRA bayan ƙarin kuɗin litar mai
- Shehu Sani ya soki matakin da PPPRA ta dauka na yin ƙarin farashin fetur
- Tsohon Sanatan na Jihar Kaduna ya ce mutane su na fama a wannan lokaci
- ‘Dan siyasar ya zargi Gwamnati da nuna rashin imani da ma rashin tausayi
A cikin tsakiyar makon nan ne gwamnatin tarayya ta bada sanarwar da bai yi wa mutane da-dama dadi ba, na cewa an samu canji a farashin litar man fetur.
Hukumar PPPRA mai kula da farashin kayan mai a Najeriya ta bada shawarar a ƙara kuɗin litar man fetur zuwa tsakanin N140.8 da kuma N143.8 a watan Yuli.
Ganin yadda man fetur ya yi tsada a halin yanzu, mutane sun fito su na kokawa da wannan mataki da gwamnati ta ɗauka bayan ɗanyen mai ya fara daraja a kasuwa.
Daga cikin wadanda su ka yi tir da wannan ƙari da aka yi har da tsohon Sanata Shehu Sani, wanda ya ce akwai rashin imani da rashin tausayi a matakin gwamnatin.
KU KARANTA: Gwamnan Anambra ya yabawa Buhari a kan nadin Shugaban NBTE

Asali: UGC
Shehu Sani ya soki wannan ƙari ne a shafinsa na Twitter, hakan ya jawo wasu sun fito sun nuna goyon bayansu da ƙarin, yayin da wasu kuma su ke sukar lamarin.
Fitaccen ɗan siyasar ya rubuta: “Ƙarin da hukumar PPPRA na kasa ta yi a kan farashin kayan mai abin ayi Allah-wadai ne, babu tausayi…”
Kwamred Shehu Sani ya cigaba da cewa: “…Kuma ba a nuna imani ba ganin irin wahalar da mutane su ke ciki a watanni biyar ɗinnan da su ka shuɗe.”
Sani ɗan gwagwarmaya ne wanda ya saba fafatuka wajen kare haƙƙin Talakawa da marasa ƙarfi a Najeriya, musamman kafin ya shiga harkar siyasa gadan-gadan.
A watanni biyar da su ka wuce, gwamnati ta ƙara haraji, sannan an rufe wuraren aiki da kasuwanci a jihohi a dalilin annobar COVID-19 da ta barke a kasashen Duniya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng