Rundunar soji ta fadi hukumomin da ke da alhakin bayyana ma su daukar nauyin Boko Haram

Rundunar soji ta fadi hukumomin da ke da alhakin bayyana ma su daukar nauyin Boko Haram

A yau, Alhamis, ne rundunar sojin Najeriya ta ce ba alhakinta ba ne gudanar da bincike tare da tona asirin ma su daukan nauyin kungiyar Boko Haram da takwararta ISWAP (Islamic State of West Africa).

A cewar rundunar soji, aikinta shine murkushe dukkan wasu 'yan ta'adda ba binciken hanyoyin da su ke samun kudi ko tallafi ba.

Shugaban sashen yada labaran atisayen rundunar soji, Manjo Janar John Enenche, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai.

A cewarsa, alhakin hukumar leken asiri ta kasa (NIA) da hukumar jami'an tsaro na farin kaya (DSS) ne su gudanar da bincike tare bayyana sunayen ma su daukar nauyin kungiyoyin ta'addanci da ke kasar nan.

"Idan aka yi la'akari da irin makaman da 'yan ta'addar su ke amfani da su, mun san akwai ta hanyar da su ke samun kudi ma su nauyi, nawa su ke samu daga dukiyar da suke sata?.

"Amma, kamar yadda na fada a baya, alhakin rundunar soji shine ta samu galaba a kan ta'addanci da duk wasu kungiyoyin 'yan ta'adda, wannan shine aikin da mu ke yi.

"Mu na da hukumar leken asiri ta kasa (NIA) da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), alhakinsu ne su yi bincike domin samun bayanai tare da bankado ma su daukan nauyin 'yan ta'adda, ba aikin rundunar soji ba ne," a cewar Enenche.

Rundunar soji ta fadi hukumomin da ke da alhakin bayyana ma su daukar nauyin Boko Haram
Manjo Janar Enenche
Asali: Original

A ranar Laraba ne rundunar sojin Najeriya ta ce babban hafsan rundunar sojojin kasa, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya ziyarci jihar Katsina domin gani da shaida irin shirin da sansani da bataliyar soji su ka yi na yaki da 'yan bindiga.

A cewar rundunar soji, Buratai bai koma Katsina ba saboda yawaitar hare - haren 'yan bindiga a jihar da jihohin Sokoto da Zamfara.

DUBA WANNAN: Katsina: Buratai ya bayyana matsayin rundunar soji a kan yin sulhu da 'yan bindiga

Ana tsammanin Buratai zai kasance a jihar Katsina na tsawon lokacin bikin ranar sojoji wanda za a fara ranar Laraba, 01 ga wata, har zuwa ranar Litinin, 06 ga watan Yuli.

A baya Buratai ya shirya yin bikin ne a Jos, babban birnin jihar Filato, amma daga baya ya sauya zuwa jihar Katsina domin karawa dakarun soji karfin gwuiwar yaki da 'yan bindiga da sauran 'yan ta'adda da ke jihohin arewa maso yamma.

Tuni kwalliya ta fara biyan kudin sabulu a atisayen 'Sahel Sanity' da rundunar soji ta kaddamar a yankin arewa ma so yamma.

Kaddamar da atisayen da rundunar soji ta yi ba zai rasa nasaba da umarnin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar na kawo karshen 'yan ta'adda da aiyukan ta'addanci a jihohin arewa ma so yamma, musamman Katsina, Sokoto da Zamfara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng