A kan tsintsiya: Dan masu gida ya sokawa 'yar haya wuka

A kan tsintsiya: Dan masu gida ya sokawa 'yar haya wuka

Wani mutum mai matsakaicin shekaru mai suna Babangida Eluemuno, ya shiga hannun 'yan sanda bayan ya kashe wata 'yar kasuwa a gidansa da ke lamba 9, titin Agba da ke garin Onitsha a jihar Anambra.

Marigayiyar mai suna Arinze Omeh, matashiya ce daga Enugwu-Ezike a karamar hukumar Igbo-Eze ta jihar Enugu.

A yayin bayyana yadda abun ya faru, Oluchukwu Omeh, dan uwan Arinze, ya sanar da manema labarai cewa a ranar Talata ne rigimar ta barke tsakanin 'yar uwarsa da dan mai gidan hayar da suke.

Ya ce, "A ranar mun dawo gida tare da Arinze bayan zuwanmu kasuwa. A yayin da nake zaune a farfajiyar gidan ina tattaunawa da makwabta.

"Babangida ya fito daga daki inda yake ce mata ta daina amfani da tsintsiyar sharar tsakar gida wurin share dakinmu.

"A martaninta, Arinze ta ce wa Babangida ta ji saboda ya saba yi mata irin wannan jan kunnen, lamarin da yasa ya cakumota.

"A kokarin ceton Arinze daga cakumar ne Babangida ya yi amfani da fasassar kwalba ya soka mata a hannu. Bayan yunkurin hana fitar jinin, Babangida ya dauko wuka."

Kamar yadda yace, ya nemo shatar adaidaita sahu da gaggawa inda suka garzaya asibiti amma sai aka ki karbarta saboda jinin da ke ta zuba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Haruna Mohammed ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce ana bincikar lamari.

A kan tsintsiya: Dan masu gida ya sokawa 'yar haya wuka
A kan tsintsiya: Dan masu gida ya sokawa 'yar haya wuka. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Na yi mafarkin idan na yi wa yarinya karama fyade zanyi kudi - Wanda ake zargi

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da damke wata budurwa mai shekaru 24 a yayin da take kan hanyar zuwa birne cikin da aka zubar mata.

Budurwar mai suna Chidera Nwaoga, an kama ta ne wurin karfe 9 na dare a kauyen Ofianta da ke Nsugbe a ranar 20 ga watan Yunin 2020, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra, Haruna Mohammed, ya ce an damke wanda ya zubar da cikin, mamallakin wani dakin shan magani ne.

Ya bayyana cewa, "A ranar 20 ga watan yunin 2020 wurin karfe 9 na dare, jami'an 'yan sanda tare da hadin guiwar 'yan banga sun kama wata Chidera Nwaoga a kauyen Nsugbe mai shkaru 24.

"An kama 'yar asalin karamar hukumar Izzi ta jihar Ebonyi dauke da diya mace wacce bata gama girma ba a mahaifa cikin bokitin roba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel