Boko Haram: Ku kawo mana agaji – Wadanda ke tsare sun roki Gwamnati
Ma’aikatan bada agaji hudu da wani mai gadi guda da su ka fada hannun ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun fito su na rokon gwamnatin tarayya da kungiyoyinsu, su kawo masu ceto.
Wadannan Bayin Allah sun yi wannan kira ne a wani bidiyo da kungiyar Boko Haram ta fitar.
A wannan faifen bidiyo mai tsawon mintuna uku da dakika 37, an ga wadannan ma’aikata da ke tsare su na kira ga hukumomi da gwamnati su ceto su daga hannun ‘yan ta’addan Boko Haram.
Daga cikin ma’aikatan da aka cafke har da masu aiki da kungiyoyin Action Against Hunger da Rich International, International Rescue Committee, da kuma wani jami’in gwamnatin Borno.
Wannan bidiyo ya shiga hannun jaridar Daily Trust kamar yadda mu ka samu labari a ranar Litinin, 29 ga watan Yuni, 2020.
Ga abin da ma’aikatan su ke fada a sakon neman daukin:
“Sunana Abdulrahman Babagana.”
“Ni ne jagoran hukumar bada agaji na SEMA a garin Monguno.”
“Na bar Monguno, a kan hanyar mu zuwa Maiduguri aka cafke ni. A ranar su ka tafi da ni zuwa sansaninsu. Yanzu ina hannunsu.”
“Ina rokin gwamnati ta ceto mu daga wannan hali.”
“A ranar 1 ga watan Yuni mu ka ci karo da su, kuma yanzu da na ke magana yau 21 ga wata (na Yuni).”
“Ku taimako ku zo ku cece ni.”
KU KARANTA: An yi bikin yaye Sojojin da za su yi maganin rashin tsaro
Shi ma Abdulrahman Dungus wanda ke tare da ‘Rich International’ ya fito ya na cewa wasu Sojojin Khalifa ne su ka kama shi a kan hanyarsa ta zuwa garin Monguno.
“Ina rokon kungiyata, ta yi abin da za ta iya, ta cece ni daga wannan wuri.” Ya na roko.
Shi kuma wani Mai gadi mai suna Joseph Prince, cewa ya yi: “Ni ma’aikacin kamfanin tsaro na Alje Security ne.”
Shi ma ya roki a kawo masa dauki, a raba shi daga hannun ‘yan ta’addan da su ke tsare da shi na kusan wata guda.
Ishaiku Yakubu, wanda jami’i ne da kungiyar ‘Action Against Hunger’ a jihar Borno ya ce:
“A ranar 8 ga watan Yuni, 2020, sojojin Khalifa su ka tare mu a kan hanyar komawa Maiduguri daga Monguno.”
Luka Filubus da ke aiki da kungiyar ‘International Rescue Committee’ a Munguno ya fito ya na cewa:
“A ranar 8 ga watan Yuni, 2020, na baro Monguno zuwa Maiduguri, sai na hadu da sojojin Khalifa.”
“Ina rokon IRC su zo, su ceci ni daga hannun sojojin Khalifa.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng