Kotu ta yanke wa barawon mota 'mai mabudin sihiri' shekaru 5 a gidan maza

Kotu ta yanke wa barawon mota 'mai mabudin sihiri' shekaru 5 a gidan maza

- Wata kotun majistare da ke Ile-Ife ta yankewa wani mutum mai suna Oga Joseph hukuncin shekaru biyar a gidan gyaran hali

- Mai shari'a Muhibah Olatunji ta kama shi da laifin satar motoci inda yake amfani da 'mabudin sihiri' wurin aika-aikar

- Alkalin ta ce bashi masauki a gidan gyara hali zai sa ya sauya tare da koyon sana'a, hakan zai kuma zama izinah ga 'yan baya

Wata kotun majistare da ke jihar Osun a ranar Alhamis ta yankewa Oga Joseph mai shekaru 21 hukuncin shekaru biyar a gidan gyaran hali a kan yin amfani da 'mabudin sihiri' wurin bude motocin jama'a.

Mai shari'a Muhibah Olatunji ta kama Joseph da laifukan da suka hada da sata.

A yayin rokon rangwame a gaban kotun, ya bayyana yadda yake amfani da mabudin sihiri wurin bude motoci tare da sacesu.

Olatunji ta ce sakin wanda ake zargin ba zai kara wa al'umma komai ba sai dai karin hargitsi.

Alkalin ta ce wannan hukuncin zai gyara wanda aka kama da laifin tare da bashi damar koyon sana'o'i da zai amfana da su bayan fitowa daga gidan gyaran halin sannan hakan zai zama izina ga wasu.

A don haka ne ta yankewa Joseph hukuncin shekaru biyar a gidan yari ba tare da tara ba.

Kotu ta yanke wa barawon mota 'mai mabudin sihiri' shekaru 5 a gidan maza
Kotu ta yanke wa barawon mota 'mai mabudin sihiri' shekaru 5 a gidan maza. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Abinda yasa nake son cire riga a fim - Jarumi Zahradeen Sani

Tun farko, dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Sunday Osanyintuyi, ya sanar da kotun cewa mai kare kansa ya aikata laifin a ranar 17 ga watan Yuni wurin karfe 9:10 na dare a titin Ibukun-Olu da ke Ile-Ife.

Osanyintuyi ya ce wanda aka yankewa hukuncin ya shiga wata mota kirar Honda Accord Saloon mai lamba FFE 707 AC, mallakin wani Adegboyega Ologbenla da niyyar sata.

Ya kara da cewa, wanda aka yankewa hukuncin ya sace wata jaka mai kunshe da N208,100, wayoyi biyu kirar Itel da abun caji guda daya. Jimillar kudinsu zai kai N223,100.

Mai gabatar da karar ya kara da cewa, a ranar 18 ga watan Yuni wurin karfe 1:53 a titin Ajegunle da ke Ile-Ife, ya shiga mota kirar Nissan Serena mai lamba MT 423 KJA, mallakin wani Olanrewaju David da niyyar sata.

Kamar yadda laifukan suke, sun ci karo da sassa na 383, 390, 412 da 508 na Criminal Code na jihar Osun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel