Kada mu bar jam'iyyar mu ta tarwatse - Buhari ga 'yan APC
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci 'yan jam'iyyar APC da su janye duk wasu kararrakin juna da suka shigar a kotu.
Ya yi kira garesu da su sasanta tsakaninsu tare da jan kunnen cewa fada-fadace zai iya tarwatsa jam'iyyar APC.
Shugaban kasar ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin taron kwamitin shugabannin jam'iyyar da aka yi ta yanar gizo a Abuja.
Ya jaddada cewa duk nasarar jam'iyyar za ta iya rikidewa zuwa rashin nasara. Ya shawarcesu da su mayar da hankali wurin hada kan jam'iyyar.
"Ya ku 'yan jam'iyya, wannan lokacin ne mai matukar muhimmanci ga jam'iyyarmu.
“A don haka cike da damuwa nake tsaye a gabanku yau a matsayina na shugaban kasar Najeriya wanda aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar APC," shugaban kasar yace.
Ya kara da cewa, "Matsalolin da a halin yanzu suka kunno kai a jam'iyyarmu abun damuwa ne ga kowanne dan jam'iyyar.

Asali: UGC
"A yayin da matsalolin cikin gida suka addabemu, wasu 'yan jam'iyyar sun yi karar 'yan uwansu kotu kuma ba mu san matsayin kwamitin gudanar da ayyukan jam'iyyar ba."
Shugaba Buhari ya matukar damuwa a kan yanayin shugabanci da sauyawar biyayya a jam'iyyar wacce yace ta sa jama'a na wa jam'iyyar ba'a.
Kamar yadda yace, akwai rikici tsakanin masu rike da shugabancin jam'iyyar a matakin kasa yayin da APC take tantama a kan wasu ikirarin shari'a tare da hukunce-hukunce.
KU KARANTA KUMA: Bayan rikita-rikita, Yan sanda sun bude sakatariyar APC dake Abuja
"A yayin da wadannan matsalolin suke kallonmu, akwai babban abun damuwa a yanayin shugabanci wanda dole ne a gaggauta shawo kan matsalolin kafin su kawo mana rabuwar kai," shugaban kasar ya ja kunne.
Ya kara da cewa, "abinda a yanzu muke ganin yana zuwa shine muke kira da illata kai. Wannan ba abun nadama bane kadai, abun kunya ne."
A baya mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce a sallami daukacin Majalisar NWC.
Jam'iyyar APC ta yanke wannan hukunci ne a wurin taron Majalisar NEC da ake yi yanzu haka a babban birnin tarayya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng