Guguwa ta hallaka mutum shida, ta rusa gidaje 600 a Kano

Guguwa ta hallaka mutum shida, ta rusa gidaje 600 a Kano

An samu wata guguwa mai karfi hade da ruwan sama da ta hallaka mutum shida a kananan hukumomi hudu na jihar Kano.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar SEMA, ta tabbatar da mutuwar mutum 6 da suka halaka sakamakon aukuwar guguwar da aka yi a kananan hukumomi hudu na jihar.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, musibar ta kuma janyo rushewar gidaje kimanin 600 a kananan hukumomin na cikin birni da na waje.

Babban Sakataren Hukumar, Sale Jilli, shi ne ya tabbatar da aukuwar wannan musiba a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni, cikin birnin Kano.

Jilli ya ce mutane 1,752 ne suka rasa matsugunansu sakamakon guguwar da ta yi watsi da su a cikin makon da ya gabata.

Gwamnan Kano; Abdullahi Umar Ganduje
Gwamnan Kano; Abdullahi Umar Ganduje
Asali: UGC

Ya bayyana sunayen kananan hukumomin da ibtila'in ya auku cikinsu da suka hadar da Gwale, Rimin Gado, Gwarzo da kuma Kibiya.

Ya ce a yanzu mutanen da suka rasa matsungunai sun fake ne a gidajen 'yan uwansu da makusanta.

Sakataren na SEMA ya ci gaba da cewa, mutum daya ya mutu ne a sakamakon jan da wutar lantarki ta yi masa yayin da sauran mutum biyar suka mutu sakamakon ruftawar da gini ya yi a kansu.

Legit.ng ta fahimci cewa, an samu duk mace-macen ne a karamar hukumar Gwale kadai da ke kwaryar birnin Kano.

A halin yanzu hukumar na ci gaba da kirdadon rahoton sauran kananan hukumomin da ibtila'in ya auku a cikin su inji Jilli.

KARANTA KUMA: Dawo da zirga-zirgar jiragen saman cikin gida ba za ta yiwu ba a ranar 21 ga watan Yuni - NCAA

Ya kara da cewa, hukumar ta tura da ma'aikata yankunan da musibar ta auku domin su gudanar da bincike da kuma kiyasin asarar da aka yi domin a san ta inda za a fara aikin agaji.

Ya ce: "Mun ziyarci karamar hukumar Kibiya da Rimin Gado, inda muka raba kayan agaji ga wadanda ibtila'in da ya auku domin rage musu radadin da suke fuskanta."

"Daga cikin kayan agajin da aka rarraba sun hadar da kayan abinci, buhunan siminta, rufin kwano, tabarmi, bargo, da kayan sawa."

Sai dai Jilli ya gargadin mazauna yankunan da ke da hatsarin aukuwar ambaliyar ruwa, da su guji zubar da shara a ko ina domin gudun da na sani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel