Gwamnatin Oyo ta sassauta dokar kulle, za a koma makarantu a ranar 29 ga watan Yuni

Gwamnatin Oyo ta sassauta dokar kulle, za a koma makarantu a ranar 29 ga watan Yuni

Bayan sassauta dokar kulle da gwamnatin jihar Oyo ta yi a makon nan, ta kuma ba da umarnin a buɗe makarantu domin ɗalibai su koma aji wajen ci gaba da daukan darasi.

Sai dai fa gwamnatin ta fayyace cewa, ɗaliban da suke ajin karshe a kowane matakin karatu na firamare da sakandire, su ne kadai za su koma makarantu a halin yanzu.

Ta ba da umarnin cewa, ɗaliban aji shida na makarantun firamare da kuma 'yan aji uku da 'yan aji shida na makarantun sakandire su koma ajujuwansu a ranar 29 ga watan Yuni.

Hakan ya na kunshe cikin sanarwar da babban sakataren sadarwa na fadar gwamnatin jihar Oyo, Taiwo Adisa ya fitar a ranar Litinin, 15 ga watan Yuni.

Gwamnan Oyo; Seyi Makinde
Hakkin mallakar hoto: Fadar gwamnatin Oyo
Gwamnan Oyo; Seyi Makinde Hakkin mallakar hoto: Fadar gwamnatin Oyo
Asali: Twitter

Mista Adisa ya ce an yanke shawarar hakan ne bayan ganawar Gwamna Seyi Makinde da kuma kwamitin da fadar gwamnatin jihar ta kafa domin yaki da cutar korona.

Ya kara da cewa, an sassauta dokar takaita zirga-zirga a jihar, kuma a yanzu jama'a za su iya walwalarsu tun daga karfe 4.00 na safiya har zuwa goman dare a kowace rana.

KARANTA KUMA: Harbe-harbe a fadar shugaban kasa: An saki dogarawan Aisha Buhari

Sauran shawarwari da aka cimma sun hadar da komawar dukkanin ma'aikatan gwamnati bakin aiki a fadin jihar.

Ya ce, "makarantun za su kiyaye dukkanin ka'idodin dakile yaduwar cutar korona da aka shata, tare da tabbatar da cewa an samar da wuraren wanke hannu a dukkanin makarantu, yayin da duk daliban za su sanya takunkumin rufe fuska."

"Daliban da ke muhimman ajujuwa ne kadai za su koma makarantu a karshen watan Yuni, tazarar makonni biyu kenan da gwamnatin jihar ta ke sa ran yanke hukunci a kan buɗe duk makarantu a ranar 15 ga watan Yuli."

"A wannan rana ce gwamnatin jihar za ta cimma shawarar karshe domin duba yiwuwar rukunin daliban da za su iya komawa makarantu."

Tuni dai daman an bai wa masallatai da sauran majami'u damar ci gaba da gudanar da harkokinsu na ibada tare da tabbatar da sun kiyaye dokar sanya takunkumin rufe fuska.

Sai dai har yanzu wuraren casu da sharholiya za su ci gaba da kasancewa a rufe a duk fadin jihar kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa.

A halin yanzu dai adadin mutum 507 ne kacal aka tabbatar cutar korona ta harba a jihar Oyo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel