Baraka a Jam’iyyar PDP bayan APC ta hana Obaseki sake neman takara

Baraka a Jam’iyyar PDP bayan APC ta hana Obaseki sake neman takara

Yunkurin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki na sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP ya fara kawo matsala a cikin tafiyar PDP.

Wasu manyan jam’iyyar adawar su na nuna mabanbanta ra’ayo game da kokarin mikawa gwamnan tikitin takara.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto cewa yayin da gwamnonin PDP su ke goyon bayan a ba Godwin Obaseki tikitin jam’iyya, wasu jagororin PDP a jihar Edo su na ganin cewa hakan zai bata tsarin jam’iyya.

Tsofaffin jiga-jigan PDP a jihar Edo sun fara nuna rashin jin dadinsu a game da yadda ake fifita Obaseki a wajen takarar gwamnan da za a yi.

Binciken da jaridar ta yi ya nuna cewa gwamna Ifeanyi Okowa oda sanatocin jihar Edo: Clifford Ordia da Urhoghide Aishagbonnriodion su na cikin masu kokarin ganin cewa PDP ta tsaida Godwin Obaseki a matsayin ‘dan takararta.

KU KARANTA: Tinubu ya ce babu matsala tsakaninsa da Ministan cikin gida

Baraka a Jam’iyyar PDP bayan APC ta hana Obaseki sake neman takara
Gwamna Godwin Obaseki
Asali: UGC

Manyan PDP a yankin irinsu Nyesom da Dan Orbihe ba su tsoma baki game da lamarin ba tukuna.

Ko da Godwin Obaseki ba zai samu damar neman tikiti a APC ba, har yanzu bai bayyana matsayarsa game da sauya-sheka ko matakin da zai dauka.

Kafin Obaseki ya sauya-sheka zuwa PDP, akwai sharudan da za a gindaya tsakaninsa da jam’iyyar domin a tsaida shi a matsayin ‘dan takara.

Daga cikin sharudan da za a bada shi ne: Ba Godwin Obaseki takardar zama ‘dan jam’iyya da tsaida shi a matsayin ‘dan takara ba tare da hamayya ba.

Sauran sharudan sun hada da: Phillip Shuaibu ba zai samu kujerarsa ta mataimakin gwamna ba. Babu maganar Obaseki ya koma jam’iyyar APC idan PDP ta lashe zabe.

Sannan kuma dole magoya bayan gwamnan su narke a PDP, kuma Obaseki ya tafi da ‘yan PDP a gwamnatinsa. Haka zalika ka da komawarsa PDP ta kawo rigima.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel