Mu na fuskantar hantara da cin zarafi a filayen jirgi - Sadiq Abacha

Mu na fuskantar hantara da cin zarafi a filayen jirgi - Sadiq Abacha

Dan marigayi tsohon shugaban kasa Sani Abacha, Sadiq Abacha, ya ce duk da dage takunkumin hana iyalan Abacha tafiye-tafiye da aka yi a zamanin Yar'adua, suna fuskantar hantara duk lokacin da za su fita daga kasar nan.

Ya ce: "Mun je wurin cibiyar tsaro har sun bani shaida. Amma ko kafin dokar hana walwalar nan na so zuwa Dubai, sai dai a filin jirgi aka tsare ni da tambayoyi.'

Sadiq ya sanar da hakan ne a wata tattaunawar da yayi da BBC a ranar Laraba.

A yayin da aka tambayesa yadda suke ji bayan rahoton daruruwan miliyoyin da mahaifin su ya kai turai, Sadiq ya ce abin na damunsu.

"Muna jin rahotannin kamar yadda kowa ya ke ji. Akwai dalilan da suka sa aka ajiye kudaden. Akwai wasu 'yan siyasa. Gaskiya bana jin dadi."

A kan dangatarkarsu da iyalan sauran shugabannin kasa da ke nan, Sadiq Abacha ya yi bayanin cewa baya ga iyalan Babangida da na shugaban kasa Muhammadu Buhari, sauran sun kasa rike zumunci.

"Muna da alaka mai kyau da iyalan Babangida."

Wannan hirar an yi ta ne bayan shekaru 22 da mutuwar Janar Sani Abacha.

KU KARANTA: Tsohon Dogari Al-Mustapha ya fito ya wanke Sani Abacha

Mu na fuskantar hantara da cin zarafi a filayen jirgi - Sadiq Abacha
Sadiq Abacha Hoto: The Net
Asali: Twitter

Kamar yadda yace: "Alakar mu a yanzu da sauran abokan mahaifinmu na da bada mamaki. Muna da alaka mai kyau da iyalan Janar Babangida.

"Iyalan Babangida ne kadai yanzu muke mu'amala har mu yi labarai idan mun hadu.

"Muna mu'amala da iyalan Buhari amma da na Babangida ne muke tuna baya.

"A lokacin da Yayale Ahmed yake sakataren gwamnatin tarayya, shi ya taimaka aka cire mana takunkumin hana tafiye-tafiye."

"Amma har yanzu ana tsare ni a filayen jirgi duk lokacin da zan yi tafiya. Suna cewa har yanzu muna da takunkumin.

"Mun je wurin jami'an tsaro kuma har sun bani shaidar cewa bamu ciki amma babu abinda ya canza. Ana hantararmu idan zamu shigo ko fita kasar nan.

"Babu abinda ya canza. Ko kafin dokar kullen nan, an tare ni ina dawowa daga Dubai." Inji sa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng