Karin mutum 260 sun kamu da korona a Najeriya

Karin mutum 260 sun kamu da korona a Najeriya

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 260 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.49 na daren ranar Lahadi 7 ga Yuni na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 260 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

Abia-67

FCT-40

Lagos-38

Ogun-19

Gombe-16

Edo-14

Imo-9

Kwara-8

Katsina-8

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Nasarawa-8

Borno-8

Kaduna-6

Bauchi-5

Ekiti-4

Niger-2

Ondo-2

Plateau-2

Kano-2

Sokoto-2

Alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Lahadi 7 ga Yunin shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 12486.

An sallami mutum 3959 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 354.

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi martani a kan zargin wasu gwamnonin jihohi da ake yi da tura wa hukumar NCDC da ake da samfur amma suna rage yawan masu cutar.

Gwamnan ya ce akwai kamshin gaskiya a wannan ikirarin. Gwamnan ya yi martanin nan ne a daya daga cikin wallafar Jibrin Ibrahim, a shafin twitter.

Ya zargi rashin gaskiya a alkalumman NCDC na masu cutar da take fitarwa a kowanne yammaci.

Ibrahim ya zargi wasu gwamnonin inda suke tura samfur kadan ga NCDC don rage yawan masu cutar korona a jihar don dawowar al'amuran walwala a jihohin.

"Wasan lambobi na kowanne yammaci da NCDC ke saki. Me kuke tunani? Ana karbar samfur ne daga dakunan gwaji na kowacce jiha wanda gwamnan jihar ke kula da shi.

"Wanda ke kula da samfur kuwa shi zai iya juya lambobin. Gwamnonin na son kananan lambobi," ya wallafa.

A kan wannan wallafar, gwamnan jihar Kaduna ya yi martanin cewa ba dukkan gwamnonin ke yin haka ba.

Kamar yadda yace, babban birnin tarayya, Kaduna da Legas na kokarin bankado dukkan masu cutar.

Ya wallafa: "Akwai kamshin gaskiya a wannan zancen. Amma ba dukkan jihohi ke fitar da lambobi kadan ba.

Babban birnin tarayya, Kaduna da Legas duk suna kokarin fitar da masu cutar saboda muna son dakile cutar.

"Muna son tseratar da rayukan jama'armu. Bamu son samun mace-macen da basu da bayani gamsasshe."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel