Rigimar APC: Jami’ai sun kama Injiniya Jubrin Imam a Jihar Neja

Rigimar APC: Jami’ai sun kama Injiniya Jubrin Imam a Jihar Neja

- Ana zargin Shugaban APC a Jihar Neja da laifin wawurar kudin Jam’iyya

- Wannan ya sa aka cafke Mohammad Jubrin Imam a Ranar Talata da rana

- Shugaban APC na Neja ya kwana ana yi masa tambayoyi kafin ya fito yau

Yanzu nan mu ke samun labari daga Daily Trust cewa rikicin da ya barke a jam’iyyar APC ta reshen jihar Neja ya kai intaha bayan an kai ga cafke shugaban jam’iyyar mai-mulki.

Jaridar ta ce an kama Injiniya Mohammad Jubrin Imam a farkon makon nan, inda ake zarginsa da laifin cin kudin jam’iyyarsa. Rahotanni sun ce kawo yanzu dai an saki shugaban.

An cafke Jubrin Imam ne a ranar Talata, 2 ga watan Yuni, 2020. An kuma sake shi ne a yau Laraba. Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC a jihar Neja ya tabbatar da wannan.

Idris Abinni ya shaidawa ‘yan jarida cewa shugaban APC na jihar ya na barci dazu. Abinni ya ce Jubrin Imam ya na hutawa ne bayan ya kwana a tsare a hannun jami’ai jiya (Talata).

KU KARANTA: Gwamna Obaseki ya hallara ofishin Jam'iyyar APC a Abuja

Rigimar APC: Jami’ai sun kama Injiniya Jubrin Imam a Jihar Neja
Jami'an 'Yan Sanda Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Jaridar ta ce ta yi kokarin tuntubar shugaban APC na reshen jihar Nejan, amma lamarin bai yiwu ba. Ana sa ran da zarar Jubrin Imam ya farka, zai yi magana game da zargin.

Legit.ng ba ta da cikakken labarin laifin da ake zargin Mohammad Jubrin Imam da aikatawa. Haka zalika jami’an tsaro da EFCC ba su iya yin magana a game da rahoton ba.

A jiya Talata, mun samu labari cewa Jubrin Imam ya yi magana da ‘yan jarida inda ya nuna cewa ba za su bari wasu 'yan taware su raba kan jam’iyyar APC mai mulki a jihar ba.

Sai dai babu shakka ana samun matsala tsakanin gwamnatin Neja ta APC da jam’iyyar. A jiyan, shugaban na APC ya tabbatar da cewa abubuwa ba su tafiya daidai tsakaninsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel