Yanzu-yanzu: Kotu tayi watsi da karar zargin da akewa tsohon shugaban Kwastam, Dikko Inde, na almundahanan N1.1bn

Yanzu-yanzu: Kotu tayi watsi da karar zargin da akewa tsohon shugaban Kwastam, Dikko Inde, na almundahanan N1.1bn

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta yi watsi da tuhumar zargin almundahanar N1.1bn da hukumar ICPC ta shigar kan tsohon shugaban hukumar kwastam, Abdullahi Dikko Inde.

Hukumar yaki da rashawar ta shigar da Dikko Inde da wasu abokan harkallarsa guda biyu ne a shekarar 2019.

Alkali Ijeaoma Ojukwu, a hukuncin da ta yanke ranar Laraba, tayi watsi lamarin saboda karar mai lamba FHC/ABJ/CR/21/2019 da lauyan ICPC, E.A Sogunle, ya shigar na janye tuhumar.

Sogunle ya bayyanawa kotun cewa duk da cewa an alanta neman Dikko Inde ruwa a jallo saboda yaki halartan zaman kotu, hukumar ta gaza kama shi har yanzu, saboda haka hukumar ta janye.

An shigar da Dikko inde kotun ne tare, Garba Makarfi, babban tsohon jami'in kwastan mai lura kudi da Umar Hussaini, lauya.

An zargesu da baiwa shugaban kamfanin Cambial Limited, Yemi Obadeyi, cin hanci don ya biya N1.1 billion (N1,100, 952,380.96) cikin asusun ofishin lauyan da sunan kudin sayan gidaje 120 ga jami'an hukumar Kwastam.

An ce Hussaini ya raba kudaden cikin asusunan banki daban-daban, kuma shi aka biyashi la'adan $3 million.

Wannan ba shi bane karo na farko da Dikko Inde zai tsallake rijiya da baya ba a kotu. A ranar Litinin, 25 ga watan Nuwamba, kotu ta dakatar da hukumar EFCC daga gurfanar da Abdullahi Inde Dikko, tsohon shugaban hukumar kwastam.

Dikko na fuskantar zargi a kan wasu makuden kudade ne da ya waskar tun yana shugabantar hukumar.

An gano cewa, kotun ta haramtawa EFCC gurfanar da Dikko saboda yarjejeniyar da suka yi da ministan shari'a da shugaban hukumar jami'an tsaro ta farin kaya, a kan cewa zai mayar wa gwamnatin tarayya dala miliyan takwas.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, tsohon shugaban hukumar kwastam din ya cika alkawarinsa don ya mayar wa da gwamnantin tarayya 1,576,000,000 ta asusun samo kudade na EFCC da ke babban bankin Najeriya.

A don haka ne mai shari'ar ya jaddada cewa, hukumar yaki da rashawa ta EFCC ko ire-irenta a fadin kasar nan ba zasu gurfanar da Abdullahi Dikko Inde ba a kan makamancin laifin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel