Sanatoci sun tabbatar da Dankaka a matsayin Shugabar hukumar FCC

Sanatoci sun tabbatar da Dankaka a matsayin Shugabar hukumar FCC

A ranar Talata, 2 ga watan Yuni, 2020, majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da Dr. Muheeba Farida Dankaka a matsayin shugabar hukumar raba dai-dai ta kasa watau FCC.

Majalisa ta amince da mukamin da shugaban kasa ya ba Farida Dankaka da wasu mutane 36 a hukumar da ke da alhakin ganin an yi adalci wajen raba arzikin kasa da mukami.

‘Yan majalisar kasar sun yi na’am da wannan mataki ne bayan sun yi la’akari da wani rahoto da shugaban kwamitin da ke lura da aikin hukumar, Danjuma La’ah ya gabatar dazu.

Bisa dukkan alamu kwamitin sanata Danjuma La’ah mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP ya yi na’am da wadannan nadin mukamai da shugaban kasar ya yi.

A ranar 18 ga watan Maris, 2020, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikowa majalisar dattawa takarda, ya na neman a tabbatar masa da nadin wadannan mutane a FCC.

Wannan zabi da fadar shugaban kasa ta yi ya jawo ce-ce-ku-ce inda wasu su ka nuna adawar su da zaben Muheeba Farida Dankaka da aka yi a matsayin sabuwar shugabar hukumar.

KU KARANTA: Buhari: Majalisa sun yi na'am da karbo aron kudi a Najeriya

Sanatoci sun tabbatar da Dankaka a matsayin Shugaban hukumar FCC
Sanata Ovie Omo-Agege Hoto: The Sun
Asali: Depositphotos

Sanata Enyinnaya Abaribe ya na cikin wadanda su ka tado wannan magana wajen tantance Dr. Muheeba Dankaka. A cewarsa bai kamata ‘yar yankin Arewa ta rike wannan matsayi ba.

Shugaban marasa rinaye a majalisar dattawa, Enyinnaya Abaribe ya ce ba a saba ganin yanki guda a Najeriya ya rike kujerar shugaba da kuma sakatare a lokaci guda a hukumar ba.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege ya mike ya kare shugaban kasar, ya ce fadar shugaban kasa za ta gyara wannan ba daidai ba da aka samu daga bangarenta.

Sanata Omo-Agege ya yarda Enyinnaya Abaribe ya na da gaskiya, ya kuma yi alkawarin za a sauya nadin da zarar wa’adin sakataren hukumar mai-ci ya cika a farkon shekarar 2021.

Wannan shi ne ra’ayin kungiyar Afenifere mai kare hakkin Yarbawa a Najeriya. kungiyar ta zargi shugaban kasa da fifita yankinsa tun a lokacin da ya aikowa majalisa sunan Dankaka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng