Katsina: 'Yan bindiga sun sake kashe mutane a sabbin harin da su kai ranar Asabar

Katsina: 'Yan bindiga sun sake kashe mutane a sabbin harin da su kai ranar Asabar

'Yan bindiga sun kashe mutane uku a kauyen Matseri da ke yankin karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Yayin harin da 'yan bindigar su ka kai a daren ranar Asabar, sun raunata karin wasu mutane 6 tare da lalata dukiyar jama'a.

A cewar mazauna yankin, 'yan bingar sun kai hare - hare a kan babura a kauyuka uku da su ka hada da Yan Nasarawa, Unguwar Alhaji Babba, da Unguwar Kanya a karamar hukumar Faskari.

Mzauna yankin sun ce 'yan bindigar sun yi awon gaba da dabbobin jama'a a kauyukan da su ka kai hare - haren.

Sai dai, da gidan talabijin na Channels ya tuntubi, SP Gambo Isah, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ya ce labarin kai hare - haren bai zo ma sa ba.

Mazauna kauyukan sun bayyana cewa sun binne jama'ar da aka kashe yayin da wadanda su ka samu raunuku ke cigaba da samun kulawa.

Harin na zuwa ne bayan kwana daya kacal da kashe mutane 13 a wani hari da 'yan bindigar su ka kai a kauyukan Unguwar Gizo, Maigora, Sabon Layi, da Mai Ruwa a karamar hukumar Faskari.

Katsina: 'Yan bindiga sun sake kashe mutane a sabbin harin da su kai ranar Asabar
Gwamnan jihar Katsina yayin sulhu da 'yan bindiga
Asali: Twitter

DSP Isah ya tabbatar da kwace shanu 130, tumaki 225 tare da kama wasu manyan gagararrun 'yan bindiga 6 da su ka addabi sassan karamar hukumar Dutsinma.

Ya ce biyu daga cikin 'yan bindigar sun fito ne daga kauyen Shamushalle, biyu daga kauyen Nahuta, yayin da ragowar biyun su ka fito daga karamar hukumar Kurfi da Safana.

DUBA WANNAN: Masana sun nuna damuwa a kan raguwar adadin ma su kamuwa da korona a Kano

Sabbin hare - haren da 'yan bindiga ke kaiwa a jihohin Katsina da Sokoto a 'yan kwanakin baya bayan nan sun yi sanadiyyar asarar rayukan jama'a da dama tare da raba muttane fiye da 5,000 da gidajensu.

Hare - haren 'yan bindigar sun cigaba da faruwa hatta a cikin wannan lokaci da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bawa rundunar tsaro ta kasa umarnin kawo karshen aiyukan 'yan ta'adda a jihohin arewa maso yamma, musamman Katsina da Sokoto.

Ko a cikin makon jiya sai da 'yan bindiga suka yi wa wasu mutane yankan rago tare da kashe wasu mutanen fiye da 60 yayin wasu hare - hare da su ka kai a kauyukan jihar Katsina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel