Mary Yakubu: ‘Yan Sanda sun cafke ‘Yar shekara 40 da ‘Ya ‘yan mutane a Taraba

Mary Yakubu: ‘Yan Sanda sun cafke ‘Yar shekara 40 da ‘Ya ‘yan mutane a Taraba

Jaridar Daily Trust ta fitar da dogon rahoton wata mata mai shekaru 40 da jami’an ‘yan sanda su ka damke ta yayin da ta ke kokarin tserewa da kananan yara 23 zuwa wani wuri a boye.

Wannan Baiwar Allah, Mary Yakubu, asalinta mutumiyar kauyen Maraban Baissa ce da ke karamar hukumar Donga, jihar Taraba, kuma ta na aiki a matsayin malamar makaranta.

Mary Yakubu ta amsa laifinta da kanta a gaban ‘yan sanda a garin Jalingo, ta shaidawa ‘yan jarida cewa iyayen yaran nan ne su ka damka mata ‘ya ‘yan na su domin a sa su a makaranta.

Kakakin ‘yan sandan Taraba, DSP David Misal, ya bayyana cewa an kama matar ne da maza 14 da mata 8. Mutanen gari ne su ka sanar da jami’ai bayan ganinta da tarin kananan yara.

Yakubu ta fallasa kanta, inda ta bayyana cewa kwanaki ta sato wasu yara 10 a wani kauye. Da aka bincika sai aka gano cewa ta kan yi wa iyaye karyar za ta sa yaransu ne a makaranta.

KU KARANTA: Alkalin kotu ya ce a rataye wasu gawurtattun ‘Yan fashi 2 a Osun

Bayan wadannan yara 23 da aka kama wannan mata da su, an kuma yi nasarar ceto wasu yara 49 da ta yi gaba da su. Jaridar ta ce hakan na nufin yara har 72 aka samu a hannun ta.

Yanzu wannan magana ta koma hannun gwamnatin Taraba, kuma jihar ta dauki nauyin ajiye yaran a wani otel da ake kira Jalingo Motel, ana daukar dawainiyar cinsu da shansu.

Ma’aikatar kula da harkar mata ta Taraba da ta ke da alhalin kula da maganin yarar ta shaidawa jaridar cewa gwamna Darius Ishaku ya kafa kwamiti da zai binciko duk iyayen yaran.

Bugu da kari gwamnatin Ishaku za ta gina makarantu da asibitoci da shaguna tare da titi a wadannan yankuna da aka shiga aka sace masu yara, kawo yanzu shirin ya yi nisa.

Gwamnatin Taraba za ta kuma fara kokarin wayar da kan mutane game da illar mikawa jama’a ‘ya ‘yansu ba tare da sun san su ba. Ta haka ne aka tserewa da ‘ya ‘ya, a nema su a rasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel