Rafia Arshad ta zama Alkalin da ke amfani da Hijabi a kotun Kasar Ingila

Rafia Arshad ta zama Alkalin da ke amfani da Hijabi a kotun Kasar Ingila

- Raffia Arshad, Lauyar da ta zama Alkali a Birtaniyya ta kafa wani sabon tarihi

- Sabuwar Alkalin ce mace ta farko da za ta yi amfani da hijabi a kotun Birtaniya

- Alkalin ta sha alwashin amfani da damar ta wajen karbowa duk mata hakkinsu

Mun samu labarin wata Baiwar Allah Musulma daga jaridar Independent da ta bar tarihi a Birtaniya, inda ta zama alkalin farko mai yin lullubi da hijabi a kaf kotun da ke Ingila.

Wannan alkali mai suna Raffia Arshad mai shekara 40 ta shafe shekaru kimanin 17 a matsayin lauya mai kare jama’a. Yanzu an kara mata matsayi zuwa mataimakiyar alkalin kotu.

Arshad za ta rika sauraron shari’a ne a wani kotu da ke shiyyar Midlands da ke tsakiyar kasar Ingila. Alkalin ta ce ta san wannan kujera ya na nufin duk musulmai sun samu murya.

Ta ce: “Kujerar ta fi karfina a karan kai na, na san cewa ba ta ni kadai ba ce. Ta na da amfani ga dukka mata, ba matan musulmai kawai ba, ta na da muhimmanci ga matan musulman.”

KU KARANTA: Wani babban Basarake ya kwanta dama a kasar Kano

Rafia Arshad ta zama Alkalin da ke amfani da Hijabi a kotun Kasar Ingila
Rafia Arshad Hoto: The Independent
Asali: UGC

A wata hira da aka yi da ita, Raffia Arshad ta ce a baya ta yi ta jin tsoron cewa ganin ta fito daga mutanen da ba su da rinjaye a al’umma, hakan zai iya kawo mata cikas a wajen aikin ta.

Sabuwar alkalin ta ce za ta yi amfani da kujerarta wajen ganin kowa ya samu adalci a kotu duk da banbancin da ake da su. Kawo yanzu ta ce ta na samun sakonni masu kara karfin gwiwa.

A shekarar 2002 ne Raffia Arshad ta fara aikin lauya a Ingila, bayan shekaru biyu kuma ta samu aiki da lauyoyin St Mary’s Family inda ta rika kare hakkin yara, mata, da kuma musulmai.

A shekarun da ta yi ta na aikin lauya, Arshad ta rika tsayawa matan da aka yi wa kaciya da kuma sauran musulmai. Duk da kokarinta, wasu su na yi mata kallon tafinta idan an shiga kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel