'Yan sanda sun kama wata mata da ta kashe mijinta a irin salon Maryam Sanda

'Yan sanda sun kama wata mata da ta kashe mijinta a irin salon Maryam Sanda

Wata matar aure ta fada komar rundunar 'yan sanda a jihar Delta bisa zarginta da kashe mijinta ta hanyar caka ma sa wuka yayin da ya ke bacci, kamar yadda Maryam Sanda ta aikata ga mijinta, Bilyaminu.

Matar ta kashe mijinta mai suna Uzougbo Iwebunor a ranar 15 ga watan Mayu a yankin Issele-Uku da ke karamar hukumar Aniocha ta arewa a jihar Delta.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Delta, DSP Onome Onovwakpoyeya, ya shaidawa manema labarai a Asaba, babban birnin jiha, cewa su na tsare da matar a hedikwatar 'yan sandan jihar.

"Ina mai tabbatar mu ku da cewa mu na tsare da matar da ake zargi da kashe mijinta.

"Sai dai, ba mu san abin da ya faru har ya kai ga ta kashe mijin nata ba.

"Rundunar 'yan sanda ta fara bincike a kan lamarin domin gano musabbabin aikata laifin kisan," a cewar Onovwakpoyeya.

'Yan sanda sun kama wata mata da ta kashe mijinta a irin salon Maryam Sanda
'Yan sanda sun kama wata mata da ta kashe mijinta a irin salon Maryam Sanda
Asali: Facebook

Henry Iwebunor, dan uwa ga mamacin, ya zargi matar da kashe dan uwansa ta hanyar caccaka ma sa wuka yayin da ya ke bacci.

"Na yi mamaki a lokacin da aka kirani tare da sanar da ni cewa dan uwana ya mutu da tsakar dare.

DUBA WANNAN: Korona: Bidiyon yadda wata mata ta cika da murna bayan an ba ta gado a cibiyar killacewa

"Saboda na san lafiyarsa kalau, sai na tambayi matarsa mene ne ya kashe shi, sai ta ce min wai haka kurum ya tashi daga bacci a firgice, ya buga kansa a jikin karfen gado, lamarin da ya sa ya fadi sumamme.

"Akwai shaidu da ke nuna cewa an kashe shi ne ta hanyar caccaka ma sa wuka, akwai raunukan sukar wuka a wuyansa da kafadarsa.

"Kafin faruwar lamarin, na san akwai rashin jituwa tsakaninsa da matarsa a kan rubuta wasiyyar ma su cin gadonsa.

"Ta takura ma sa a kan rubuta wasiyyar, lamarin da ya haifar da yawan rikici a tsakaninsu, kamar yadda kowa ya sani a dangi," a cewar Iwebunor.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng