Mai Garin Batsari: Miyagu ke kashe mu, Coronavirus ba ta hallaka kowa ba

Mai Garin Batsari: Miyagu ke kashe mu, Coronavirus ba ta hallaka kowa ba

A halin yanzu ana cigaba da kai wa Bayin Allah munanan hare-hare a jihar Katsina. Rahotanni sun ce ana kashe jama’a, ayi garkuwa da su, har ayi wa ‘yan mata fyade a kauyuka.

A wani bidiyo da ya ke yawo a kafafen sadarwa na zamani, wani Basarake a kasar Katsina wanda mu ke zargin cewa Hakimin Batsari ne, yayi Allah-wadai da irin musibar da su ke gani.

Idan har ta tabbata Sarkin Ruman Katsina watau Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Mu’azu Ruma ne a wannan bidiyo, ya koka da cewa ta’adin miyagun da ke Katsina ya zarce na COVID-19.

Mai garin ya ke cewa cutar COVID-19 ba ta kashe kowa a yankin Batsari ba, amma kawo yanzu miyagun ‘yan bindigan da su ka addabi kauyukan Katsina, sun kashe Bayin Allah rututu.

A cewar wannan Bawan Allah kusan babu wani banbanci tsakanin annobar cutar COVID-19 da ‘yan ta’adda, har ma ya na ganin a garin Batsari, a iya cewa gara wannan mugun ciwo.

KU KARANTA: Coronavirus: Limamai sun ce El-Rufai ya fi sauran Gwamnoni kokari

“Coronavirus ba ta kashe mana ko mutum guda a karamar hukumar Batsari ba, amma wadannan ‘yan ta’adda sun kashe mana mutane da ba mu san iyakarsu ba.” A cewar Basaraken.

Da ya ke cigaba da magana game da tashin hankalin da jama’ansa su ka shiga, sai ya ce: “Menene bambancinsu (‘Yan ta’addan da ke cikin jihar Katsina) da annobar ta Coronavirus?”

A karshe ya fada, ya kuma nanata cewa: “Mu gara COVID-19 da wadannan ‘yan bindiga.” A bidiyon da mu ka gani, Mai garin ya shaidawa gidan talabijin na Channels TV ne wannan.

Duk da cewa gwamnatin jihar Katsina, ta yi sulhu da 'yan bindiga kwanakin baya, har gobe ana cigaba da hallaka mutane dare da rana a kananan hukumomi kusan 12 da ke jihar.

Tun a farkon shekarar nan ‘yan bindiga su ka addabi karamar hukumar Batsari har akwai lokacin da aka kai hari a wani asibitin kauyen. Ana zargin gwamnati da sakacin kare jama’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng