Gwamnan Neja ya sake tsawaita dokar kulle na tsawon makonni 2 a jihar

Gwamnan Neja ya sake tsawaita dokar kulle na tsawon makonni 2 a jihar

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya nuna damuwarsa da yadda mazauna jihar sa ke ta ke dokar nesa-nesa da juna don dakile yaduwar annobar coronavirus.

Bello ya sanar da hakan ne yayin jawabi ga manema labarai jim kadan bayan taron mako-mako da yake yi da mambobin kwamitin yaki da cutar korona na jihar.

"Abin takaici ne yadda muka rufe iyakokinmu tsakaninmu da wasu jihohin amma kwalliya bata biya kudin sabulu ba. Masu babura suna yawan kaiwa da kawowa wanda hakan ke nuna karantsaye ga dokar gwamnatin."

Gwamnan ya sanar da dokar hana aikin babura a jihar na makonni biyu yayin da duk sauran dokokin za su ci gaba da aiki na tsawon makonni biyun.

Gwamnan Neja ya sake tsawaita dokar kulle na tsawon makonni 2 a jihar
Gwamnan Neja ya sake tsawaita dokar kulle na tsawon makonni 2 a jihar Hoto: Channels Television
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, yayin jaddada kokarin gwamnatin na bada kariya ga ma'aikatan lafiya da kuma 'yan kwamitin yaki da cutar na jihar, Bello ya tabbatar da cewa gwamnati za ta dauka mataki mai tsauri a kan harkar ma'aikatan lafiyanta.

Gwamnan ya yi kira ga jama'a da su kiyaye tsaftar kansu, zama nesa-nesa da juna, saka takunkumin fuska idan za a shiga jama'a da kuma gaggauta neman shawarar masana kiwon lafiya yayin da wata alamar cutar ta bayyana.

"Ina kira ga jama'a da suka san sun yi tafiya zuwa jihohin da cutar korona ta isa da su tabbatar da sun killace kansu da kuma kai rahoto ga cibiyar lafiya mafi kusa."

KU KARANTA KUMA: Nesa ta zo kusa: ABU Zaria ta samo maganin cutar COVID-19

Gwamnan ya bayyana cewa jihar na kokarin ganin ta samar da dakin gwaji a babban asibitin jihar da ke Minna don kara yawan samfur din da za a dinga gwada wa a kowacce rana.

Gwamnatin jihar Neja ta bada umarnin rufe jihar a kan yunkurinta na yi wa manyan biranen jihar shida feshi.

Ya ce gwamnatin jihar ta horar da ma'aikatan lafiya 457 tare da daukar ma'aikata 20 na wucin-gadi don taimakawa a dakin gwaji.

Ya yi bayanin cewa gwamnatin an kai magunguna da kayan kariya ga cibiyoyin killacewa na jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel