Yanzu-yanzu: Asusun lamunin duniya IMF ta amince da baiwa Najeriya tallafin $3.4bn

Yanzu-yanzu: Asusun lamunin duniya IMF ta amince da baiwa Najeriya tallafin $3.4bn

Asusun lamunin duniya IMF ta amince da baiwa gwamnatin Najeriya tallafin $3.4 billion (N1.2 tiriliyan) domin yakar muguwar cuta mai toshe numfashi Coronavirus (COVID-19).

Wannan tallafi da asusun lamunin ta baiwa Najeriya shine mafi yawa da za ta baiwa wata kasa a duniya.

Asusun lamunin na bada tallafin mai suna 'Rapid Financing Instrument (RFI)' ne ga kasashe mambobin kungiyar amma basu cikin wani shirin taimako na IMF.

Yanzu-yanzu: Asusun lamunin duniya IMF ta amince da baiwa Najeriya tallafin $3.4bn
IMF ta amince da baiwa Najeriya tallafin $3.4bn
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng