Masu horas da ‘Yan wasa sun zabi Lionel Messi a gaban Cristiano Ronaldo

Masu horas da ‘Yan wasa sun zabi Lionel Messi a gaban Cristiano Ronaldo

Shekara da shekaru kenan yanzu babu wanda ake jin labarinsa a duniyar kwallon kafa illa Lionel Messi da Cristiano Ronaldo. Tun shekarar 2008 taurarin biyu su ka gagari kowa.

A cikin shekaru 12 da su ka wuce, Lionel Messi da Cristiano Ronaldo sun kasance sun lashe duk wata kyautar Ballon D’or da ake ba ‘dan wasan kwallon kafan da ya zama zakaran shekara.

A dalilin haka ake yawan tafka muhawara a kan ‘yan wasan biyu. Wasu su na ganin cewa ‘dan wasa Messi na Argentina ne gwani, yayin da wasu su ke tare da Ronaldo na kasar Portugal.

Wani rahoto da jaridar The Sun ta Ingila ta fitar ya bayyana cewa manyan sunayen da ake da su na masu horas da ‘yan kwallon kafa sun fito sun bayyana zabinsu a tsakanin ‘yan wasan gaban.

Daga cikin wadanda su ka bayyana zabinsu akwai tsofaffin masu horas da ‘yan wasan kwallo:

KU KARANTA: Katafaren gidan da Tauraro Ronaldo ya ke zaune a ciki a Mahaifarsa

Masu horas da ‘Yan wasa sun zabi Lionel Messi a gaban Cristiano Ronaldo
Har gobe gardamar Lionel Messi ko Cristiano Ronaldo ta ki ta kare
Asali: Getty Images

1. Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya zabi Cristiano Ronaldo

2. Kocin Tottenham Jose Mourinho ya zabi duka ‘yan wasan biyu

3. Tsohon Kocin Arsenal Arsene Wenger ya zabi Lionel Messi

4. Tsohon Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya zabi Cristiano Ronaldo

5. Kocin Atletico Madrid Diego Simeone ya zabi Lionel Messi

6. Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya zabi Lionel Messi

7. Kocin Manchester City Pep Guardiola ya zabi Lionel Messi

Zinedine Zidane ya yi aiki da ‘dan wasa Cristiano Ronaldo a lokacin da ya ke Real Madrid. Haka zalika Sir Alex Ferguson shi ne wanda ya fara taso da ‘dan wasan na Portugal a Manchester.

Pep Guardiola ya zabi tsohon yaronsa a Barcelona watau Lionel Messi kamar dai yadda tsohon kocin Arsenal, Arsene Wenger ya zabe sa. Wenger ya na cikin masu sha’awar ‘dan wasan.

Messi ya samu kuri’ar kocin kungiyar Atletico Diego Simeone da Jurgen Klopp na Liverpool. A lokacin da ya ke Madrid da Manchester, Ronaldo ya yi gaba da duk kungiyoyin nan biyu.

Jose Mourinho wanda ya horas da Chelsea, Inter Milan, Real Madrid da Manchester United bai da zabi tsakanin ‘yan wasan. Mourinho ya nuna bai da na-zaba tsakanin Taurarin masu tashe

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel