Yawan mace-mace: Na damu da halin da Kano ke ciki – Hadimin Buhari ya roki yan Najeriya da su yi wa birnin addu’a

Yawan mace-mace: Na damu da halin da Kano ke ciki – Hadimin Buhari ya roki yan Najeriya da su yi wa birnin addu’a

- Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Buhari, ya bukaci yan Najeriya da su sanya jahar Kano cikin addu’a

- Yayinda jahar ke gwagwarmaya da annobar COVID-19, sai kuma ga lamari na yawan mace-macen mutane daga wasu cututtuka da ba a sani ba ya kunno kai

- Ahmad ya nuna damuwa kan yawan mace-macen mutanen mai cike da al’ajabi a jahar

Biyo bayan yawan mace-mace da aka samu a jahar Kano a yayinda ake tsaka da annobar Coronavirus, wani hadimin Shugaban kasa, Bashir Ahmad, ya yi martani a kan lamarin.

Ahmad ya yi kira ga yan Najeriya da su ajiye akidar siyasa da banbancin addini a gefe sannan su yi wa jahar addu’a.

Yawan mace-mace: Na damu da halin da Kano ke ciki – Hadimin Buhari ya roki yan Najeriya da su yi wa birnin addu’a

Yawan mace-mace: Na damu da halin da Kano ke ciki – Hadimin Buhari ya roki yan Najeriya da su yi wa birnin addu’a
Source: Twitter

Legit.ng ta ruwaito cewa Ahmad wanda ya kasance hadimin shugaba Buhari na musamman a shafukan sadarwa na zamani, ya yi wannan roko ne a ranar Asabar, 25 ga watan Afrilu, ta shafinsa na Twitter, @BashirAhmaad.

An tattaro cewa wani bakon rashin lafiya na ta kashe wasu manyan mutane a jahar, sannan yayin da wasu ke nuna alamu na coronavirus, ba a san abun da ya haddasa mutuwar wasu ba.

An yi hasashen cewa zafi ne ke kashe mutane amma mazauna jahar sun ce ba za su iya bayanin abun da ke faruwa a tsohuwar birnin mai cike da tarihi ba.

A rubutun da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Ahmad ya bukaci yan Najeriya da su yi wa Kano addu’a, inda ya kara da cewar ya damu sosai a kan yawan mace-macen da ake samu a jahar.

KU KARANTA KUMA: Abba Kyari: Babu ruwan APC a wanda zai zama shugaban ma’aikatan Shugaban kasa na gaba - Issa-Onilu

Ya ce: “Na damu sosai a kan Kano. Allah SWT ya ji kan wadanda suka mutu sannan ya saka masu da Al-jannah.

"Tabbass wannan lokaci be da ba a saba gani ba. Lokaci ne da za mu ajiye duk banbancinmu, uzururruka, sannan mu hadu mu yi aiki tare a matsayin yan uwa. Ku yi wa Kano addu’a.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel