COVID-19: Budurwa roki NCDC ta kama mahaifiyarta saboda karya dokar zaman gida a Nasarawa

COVID-19: Budurwa roki NCDC ta kama mahaifiyarta saboda karya dokar zaman gida a Nasarawa

- Wata budurwa a Twitter mai suna @ruthyore ta yi amfani da dandalin sada zumunta ta bukaci a kama mahaifiyarta

- Budurwar ta sanar da Hukumar kiyayye cuttuka masu yaduwa, NCDC cewa mahaifiyarta ta tafi gidan biki

- Sakamakon bullar cutar coronavirus a wasu jihohi, gwamnatin tarayya ta saka dokar zaman gida da hana taruwa jama'a

- Mutane da dama a dandalin sada zumuntar sun bayyana mabanbantan ra'ayi game da abinda budurwar ta aikata

Duk da dokar kulle da hana yin taruwar mutane da gwamnatoci suka saka a jihohin su sakamakon bullar annobar coronavirus, wasu mutane suna cigaba da saba dokar.

Bisa dukkan alamu wata budurwa mai suna @ruthyorea a Twitter ta gaji da irin wannan saba dokar hakan yasa ta cire son rai ta dauki mataki a kai.

A sakon da @ruthyorea ta wallafa a Twitter, ta yi kira ga Hukumar kiyayye cuttuka masu yaduwa, NCDC, su taimaka su tafi inda mahaifiyarta ta tafi biki su kama su.

DUBA WANNAN: An kama mutumin da ya haike wa matarsa har ta mutu a Jigawa

A cewar ta, mahaifiyarta ta tafi bikin aure ne a Maraba da ke Nasarawa duk da dokar hana taron jamaa da aka saka a jihar.

Tana fargabar yiwuwar mahaifiyarta ta kamu da cutar coronavirus.

Ga abinda ta rubuta, "Ina kwanan ku @NCDCgov, shin ko za ku iya taimakawa su kama mahaifiyata a Maraba. Ta tafi taron biki ne a Maraba. Don Allah ku aika tawagar ku su tafi unguwar su hana taron bikin auren. Nagode."

Mutane da dama sun ta bayyana raayoyinsu game da abinda budurwar ta aikata, wasu daga cikinsu sun jinjina mata.

Wasu kuma suna ganin ta cika tsegumi yayin da wasu ke ganin ta kyauta domin tana kokarin kare lafiyarta ne da na iyalin ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel