Kano: Gwamna Ganduje ya bada umarnin bincike a kan silar mace-macen da ake a jihar

Kano: Gwamna Ganduje ya bada umarnin bincike a kan silar mace-macen da ake a jihar

Bayan samun rahoton mace-macen da aka yi a jihar Kano a cikin makon da ya gabata, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin bincike don gano sanadiyyar wannan mace-macen.

A kalla mutum 40 ne aka birne tun bayan bullar muguwar cutar coronavirus a makabartar Dandolo da ke karamar hukumar Dala ta jihar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ana samun mamata a kalla uku zuwa biyar ne a kowacce rana.

A makabartar kofar Mazugal kuwa, ana birne a kalla mutum 10 yanzu a kowacce rana, lamarin da ya tada hankulan jama'a sannan suka bukaci a bincika dalili.

Hakazalika, a makabartar Kara da ke kusa da mayanka, Aminu Koki ya sanar da jaridar cewa an birne gawawwaki 42 tsakanin ranar Litinin zuwa Talata.

Amma ya ce: "Ban san sanadin mutuwarsu ba. Lamarin da bada tsoro kuma akwai bukatar gwamnati ta saka hannu."

Kano: Gwamna Ganduje ya bada umarnin bincike a kan silar mace-macen da ake a jihar

Kano: Gwamna Ganduje ya bada umarnin bincike a kan silar mace-macen da ake a jihar
Source: Twitter

KU KARANTA: Kano: 'Yan sanda sun damke limamai 15 a fadin jihar

Shugaban kwamitin kula da makabartu na karamar hukumar Fagge, Sheriff Hadi Kabir, ya yi kira ga gwamnati da ta kawo dauki don gano sanadin rasa rayukan da ake yi a jihar.

Kabir, wanda ya rasa mahaifinsa a kwanaki uku da suka gabata, ya kwatanta lamarin da abun tsoro.

Ya ce a Zangon Barebari da ke birnin Kano, a kalla mutum 13 ne suka rasu tsakanin ranar Lahadi da Litinin sakamakon zazzabi mai zafi.

Ya danganta zazzabin da na cizon sauro wanda hakan ke faruwa sakamakon isowar damina.

Kamar yadda yace: "Wannan ba cutar coronavirus bace kamar yadda ake zargi, zazzabin cizon sauro ne saboda yawan sauro a jihar."

A yayin martani ga lamarin daga kwamishinan yada labarai, Muhammad Garba, wanda ya duba rahoton mace-macen, ya ce gwamnatin jihar ta gaggauta fara bincike a kan lamarin.

Duk da Garba ya musanta cewa ana mutuwa ne sakamakon annobar Coronavirus a jihar, ya tabbatar da cewa Gwamna Ganduje ya bai wa ma'aikatar lafiya umarnin bincikar lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel