Dakarun Najeriya sun halaka shugabannin Boko Haram a Borno

Dakarun Najeriya sun halaka shugabannin Boko Haram a Borno

- Manyan shugabannin kungiyar ta'addanci ta Boko Haram da ISWAP sun sheka lahira sakamakon ruwan wutan da dakarun Operation Lafiya Dole

- Shugaban fannin yada labarai na hedkwatar, Manjo janar John Enenche ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin a garin Abuja

- Kamar yadda yace, jiragen yakin da aka tura sun dage wajen kai harin inda suka dinga ruwan wuta ga 'yan ta'addan wanda hakan ya jawo ajalinsu

Manyan shugabannin kungiyar ta'addanci ta Boko Haram da ISWAP sun sheka lahira sakamakon ruwan wutan da dakarun Operation Lafiya Dole suka yi musu ta sama a Durbada da ke Borno, hedkwatar tsaro ta tabbatar.

Shugaban fannin yada labarai na hedkwatar, Manjo janar John Enenche ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Litinin a garin Abuja.

Ya kara da cewa hatta gine-ginen da aka san mallakin 'yan ta'addan ne an murkushesu.

Enenche ya bayyana cewa, sun kai harin ne a ranar 17 ga watan Afirilun 2020 bayan wasu bayanan sirri da suka samu, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce bayanan sirrin sun tabbatar da cewa wannan yankin ne wasu daga cikin 'yan ta'addan ke buya.

Dakarun Najeriya sun halaka shugabannin Boko Haram a Borno
Dakarun Najeriya sun halaka shugabannin Boko Haram a Borno
Asali: Facebook

KU KARANTA: Boko Haram: Shekau na kokarin mika kansa ga gwamnatin Najeriya

Kamar yadda yace, jiragen yakin da aka tura sun dage wajen kai harin inda suka dinga ruwan wuta ga 'yan ta'addan wanda hakan ya jawo ajalinsu.

"Sauran da suka yi yunkurin gudu tare da neman mafaka wasu sojin sun bi su tare da halaka su.

"Domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa maso gabas din kasar nan, sojojin za su ci gaba da harar makiyan kasar nan har sai sun kare," yace.

A wani labari na daban, shugaban 'yan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau yana tunanin yada makamai tare da mika kansa ga gwamnatin Najeriya, majiya mai karfi ta sirri daga yankin Arewa maso gabas din kasar nan ta sanar da jaridar The Vanguard.

Majiyar ta sanar da jaridar cewa, Shekau ya fara neman hanya mai sauki don mika kanshi ga gwamnatin.

Kamar yadda majiyar tace, shugaban Boko Haram din ya fara tuntubar wasu kungiyoyin taimakon kai da kai na kasashen duniya don samun ragwame daga gwamnatin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel