Coronavirus: Har yanzu ban warke ba - Gwamna El-Rufai

Coronavirus: Har yanzu ban warke ba - Gwamna El-Rufai

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bukaci alumma su yi watsi da labaran bogi da ake yadawa game da cutar COVID-19 da ta kama shi

Gwamnan jihar Kadunan ya ce har yanzu likitoci ba su ce ya warke ba saboda haka har yanzu yanan nan a killace

ElRufai wanda ya jogaranci taron kwamitin zartarwa na jihar ta naurar bidiyo a ranar Laraba ya ce shi da kansa zai sanar da yan Najeriya idan ya warke

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce har yanzu bai warke daga coronavirus da ta kama shi ba inda ya kara da cewa shi da kansa zai sanar da yan Najeriya idan ya warke.

Gwamnan jihar Kadunan ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba 15 ga watan Afrilu ta shafinsa na Facebook.

Gwamnan ya bukaci mutane su yi watsi da labaran bogi da aka wallafa wa game da rashin lafiyarsa.

Gwamnan da ya ke a killace ya jagoranci taron kwamitin zartarwa na jihar a ranar Laraba.

DUBA WANNAN: Shekau ya fadi maganin coronavirus a cikin sabon sakon sautin murya da ya fitar

Ya kara da cewa, "Ina matukar alfahari da kwamishinonin mu, masu bayar da shawara, mataimaka, hukumomin tsaro da sauran maaikata a jihar saboda jajircewarsu."

A wani rahoton, mun kawo muku cewa gwamnatin jihar Kadunan ta saki fursunoni 72 daga gidan gyaran hali a jihar da ke Kafanchan saboda rage cinkoso da kuma kare yaduwar cutar coronavirus a jihar.

Attoni Janar na jihar kuma kwamishinan Sharia, Aisha Dikko ce ta sanar da sakin fursunonin a ranar Talata 14 ga watan Afrilu.

Ta ce an saki fursunoni 69 a Kaduna yayin da aka kuma saki wasu uku a Kafanchan.

Legit.ng ta gano cewa kwamishinan ta ce 42 cikin fursunonin da aka saki daga Kaduna wadanda aka yanke musu hukunci ne kuma aka basu zabin biyan tara da bai dara 5O,OOO ba.

Dikko ta kara da cewa hudu daga cikin fursunonin an yanke musu zaman shekaru uku da abinda ya fi haka ne kuma saura watanni shida su gama zaman su na gidan yarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel