Yan sanda sun kama mutane 150 da ke da nasaba da tashe-tashen hankula a jahar Ogun
- Runduar yan sandan jahar Ogun ta kama mutane 150 da ake zargi da laifuffuka daban-daban a jahar
- Wadannan laifuffuka sun hada da fashi da makami, fashe-fashen shaguna da kuma rikici a wasu yankunan jahar
- Yan sandan sun yi kamun ne bayan jan hankalinsu da mutanen yankunan suka yi a kan hare-haren da ake kai masu
Rahotanni sun kawo cewa rundunar yan sandan jahar Ogun, ta kama akalla mutane 150 da ake zargin suna da nasaba da haddasa tashe-tashen hankula da wasu laifuffuka.
Wadannan laifuffuka sun hada da fashi da makami, fashe-fashen shaguna da kuma rikici a wasu yankunan jahar.
Legit.ng ta tattaro cewa wadannan laifukan ta’addanci sun haddasa tashin hankali a tsakanin mazauna yankunan Agbado Ijaiye, Sango, Ijoko da kuma Ifo.
An kama masu laifin ne bayan mazauna garuruwan Owode, Ilepa, Ifo, Arigbajo, Itori, Dalemo, Ijoko Joju, Sango, Ota a Ifo, Agbado-Ijaiye, a kananan hukumomin Ifo da Ado-Odo/Ota da ke jahar Ogun sun sanar da yan sanda hare-haren da ake kai masu.
KU KARANTA KUMA: An feshe wuraren da mai coronavirus ya ziyarta a Kano da magani
A wani labarin kuma, mun ji cewa an shiga tashin hankali a yankunan Mangoro, Ogba, Agege, Iyana Ipaja da kuma Dopemu da ke jahar Legas, yayinda yan ta’adda suka yiwa mazauna yankunan fashi da makami.
A wani lamari mai kama da shiryayyen aiki, an tattaro cewa yan fashin sun isa yankunan a kan babura da manyan motocin bas, dauke da makamai daban-daban.
Mazauna yankunan sun bayyana cewa barayin sun sace kayayyakin abinci a shaguna da manyan dakunan ajiya da ke yankunan, jaridar TheCable ta ruwaito.
“Sun zo da misalin karfe 7:00 na dare da babura guda 30 da manyan motocin bas guda 10,” in ji wani mazaunin Aluminium Village a Dopemu.
“An yiwa gidaje da dama da shagunan siyar da kayan abinci fashi. Sun ma fasa wasu manyan dakunan ajiya sannan suka sace kayayyakin da ke wajen.”
A yankin Mangoro, wani mazaunin wajen ya bayyana cewa mutane na unguwanni, suna yiwa mutane kwace.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng