Sabbin cibiyoyin gwajin cutar covid-19 a jihohin arewa 4 za su fara aiki a cikin satin nan - NCDC
Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta tabbatar da cewa sabbin dakunan gwajin kwayar cutar covid-19 a jihohin Kano, Kaduna, Filato da Maiduguri za su fara aiki a cikin satin nan.
Dakunan gwajin za su taimaka matuka wajen shawo kan yaduwar kwayar cutar covid-19 ta hanyar gano masu dauke da kwayar cutar ba tare da bin doguwar hanya ba.
Bashir Ahmad, mataimaki na musamman ga shugaba Buhari a bangaren kafafen sadarwa na zamani, ne ya sanar da hakan a cikin wani takaitaccen sako da ya wallafa a shafinsa na dandalin tuwita a daren ranar Litinin.
Kafin sanar da lokacin fara aikin cibiyoyin, akwai wasu cibiyoyi biyar a jihohin Najeriya uku da ke gudanar da gwajin kwayar cutar covid-19 a kan wadanda ake zargin sun kamu da kwayar cutar.
A ranar Litinin ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyara cibiyar killace masu dauke da cutar covid-19 da gidauniyar Dangote tare da hadin gwuiwar gwamnatin jihar Kano suka samar.
Cibiyar, mai jimillar gadon kwantar da marasa lafiya 509, tana da bandakuna, dakin gwaji, dakin shan magani, motar daukan marasa lafiiya, dakin ganawar ma'aikata da masana da sauransu.
DUBA WANNAN: FG ta rabawa talakawan Kano biliyan N1.6
Tun a ranar 29 ga watan Maris Legit.ng ta wallafa rahoton cewa hamshakin attajirin dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, zai samar da wata cibiyar killace wa mai gado 600 domin duba wadanda suka kamu da kwayar cutar coronvirus a jihar Kano.
Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ne ya sanar da hakan yayin kaddamar da kwamitin neman kudin taimakawa masu karamin karfi a jihar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng