Najeriya za ta talauce idan har aka cigaba da samun matsalar Coronavirus na tsawon watanni shida - Ministar kudi

Najeriya za ta talauce idan har aka cigaba da samun matsalar Coronavirus na tsawon watanni shida - Ministar kudi

Ministar kudi ta Najeriya, Zainab Ahmed Shamsuna, tayi gargadin cewa Najeriya ka iya talaucewa idan har cutar Coronavirus ta cigaba da wanzuwa na tsawon watanni shida

Ta bayyana hakane a lokacin da ta kai ziyara gidan talabijin na Channel a jiya, inda ta bayar da rahoto akan hanyoyin da ake bi wajen magance matsalar Coronavirus kada ta shafi tattalin arzikin Najeriya.

"Muna fatan wannan matsalar ba za ta dauki lokaci mai tsawo ba," cewar ministar.

Ta cigaba da cewa, "Idan har ta tsaya nan da watanni uku, babu wata matsala, amma idan har ta wuce wata uku tabbas Najeriya za ta talauce."

A cewar Zainab, gwamnatin tarayya da ta jiha za su shiga matsala a fannin samun kudin shiga, gashi kuma dama kudin danyen man fetur ya fadi a kasuwannin duniya.

Najeriya za ta talauce idan har aka cigaba da samun matsalar Coronavirus na tsawon watanni shida - Ministar kudi

Najeriya za ta talauce idan har aka cigaba da samun matsalar Coronavirus na tsawon watanni shida - Ministar kudi
Source: UGC

Ta yi bayanin cewa hakan ne ya sanya gwamnati take neman hanyar da za ta dinga samun kudin shiga domin karfafa tattalin arziki a wannan lokaci.

A kokarin da ake na kawo karshen cutar da kuma neman hanyar da za ta sanya baza ta yiwa tattalin arziki illa ba, ministar ta bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wata kwamiti da take kula da bangare na cutar.

Ta bayyana cewa kwamitin wacce ta kunshi ma'aikatu, masana'antu da kamfanoni wacce sakataren gwamnatin tarayya yake jagoranta za ta yo aiki yadda ya kamata.

Zainab kuma tayi magana akan hanyar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kawo ta taimakawa 'yan Najeriya.

Atiku ya bayyana cewa gwamnati ta bayar da naira dubu goma ga mutane miliyan talatin domin sayen kayan abinci, sannan ta rage farashin man fetur.

Haka kuma tsohon mataimakin shugaban kasar yayi kira ga gwamnati ta raba katin waya na naira dubu daya da dari biyar ga mutane miliyan dari domin kiran gaggawa.

A yayin da take mayar da martani, ministar tace tayi na'am da wannan shawara ta Atiku, amma kuma tana duba abinda ka iya zuwa ya dawo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel