Yanzu Yanzu: APC ta dage taron NEC har sai baba ya gani

Yanzu Yanzu: APC ta dage taron NEC har sai baba ya gani

- Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta dage taron msu ruwa da tsakinta da aka shirya yi a ranar Talata har sai baba-ya-gani

- Hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da aka kulla a lokacin ganawa tsakanin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jam’iyyar APC

- An dai yi ganawar ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja a yau Litinin

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an dage taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da aka shirya yi a ranar Talata har sai baba-ya-gani.

An dakatar da taron ne sakamakon yarjejeniyar da aka kulla a lokacin ganawa tsakanin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jam’iyyar APC a fadar Shugaban kasa a yau Litinin, 16 ga watan Maris.

Yanzu Yanzu: APC ta dage taron NEC har sai baba ya gani
Yanzu Yanzu: APC ta dage taron NEC har sai baba ya gani
Asali: Facebook

Da fari dai mun ji cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shiga wata ganawar sirri da gwamnonin jam'iyyar APC 16 a fadarsa gabanin taron majalisar zartarwa da ake saka ran zai yanke matsaya a kan shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, da kotu ta dakatar a amakon jiya.

Gwamnonin da suke cikin taron sun hada da na jihar Borno, Lagos, Ogun, Edo, Kebbi, Jigawa, Kwara, Nasarawa, Niger, Plateu, Ondo, Kano, Osun, Katsina, Imo da Gombe.

Daga cikin gwamonin jam'iyyar APC 20, hudu ne kawai bau halarci taron ba. Sun hada da gwamnan jihar Kaduna, Yobe, Kogi da Ekiti.

Batun yunkurin tsige Oshiomhole daga kujerarsa ya gwara kan masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC da suka hada da gwamnoni, mambobin majalisa, shugabannin jam'iyya na jihohi, mambobin kwamitin zartarwa (NWC) da sauransu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel