Yanzu Yanzu: Buhari ya isa Kebbi don halartan bikin kamun kifi na Argungu

Yanzu Yanzu: Buhari ya isa Kebbi don halartan bikin kamun kifi na Argungu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Birnin Kebbi domin halartan bikin baje kolin kayan noma, daga cikin bikin kamun kifi na Argungu na 2020.

Manyan jami’an gwamnati karkashin jagorancin Gwamna Atiku Bagudu be suka tarbi shugaban a filin jirgin sama.

Da fari gwamnatin tarayya a ranar Alhamis, 12 ga watan Maris, ta kaddamar da bikin kamun kifi na Argungu a Abuja.

Yanzu Yanzu: Buhari ya isa Kebbi don halartan bikin kamun kifi na Argungu
Yanzu Yanzu: Buhari ya isa Kebbi don halartan bikin kamun kifi na Argungu
Asali: UGC

Shugaban kasar wanda ya samu wikilcin ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed a Abuja, ya ce samar da kafar amfani da kayayyakin gida a bikin wannan shekarar ya yi bayanin manufar gwamnati kan amfani da kayayyakin da aka sarrafa a gida Najeriya.

Ya kara da cewa a shirye gwamnatin tarayya ta ke ta yi amfani da masana’antar motoci da ka iya samar da biliyoyin daloli ga kasar a duk shekara.

“Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bayar da gagarumin goyon baya da ake bukata ga bikin kamun kifi na Argungu da sauran bukukuwa a kasar a kokarinta da bunkasa fannin yawon bude ido.

“Mun jajirce domin ganin mun habbaka tattalin arziki ta fannin masana’antu da bangaren shakatawa,” in ji shi.

Ya bayyana cewa dukkanin motocin rangajin a Najeriya aka tattara su, wanda hakan na daga cikin kokarin bunkasa kamfanin motocin Najeriya.

A jawabinsa, Darakta Janar na kungiyar NDDC, Jelani Aliyu ya ce bikin kamun kifi na Argungu zai kasance fage na baje kolin motocin da aka kera a Najeiya.

A wani labari na daban, mun ji cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya musanta karbar kyautar naira miliyan 300 daga hannun jam’iyyar APC reshen jahar Bayelsa da tsohon zababben gwamnan jahar na APC, David Lyon wanda kotu ta soke nasararsa.

Jonathan ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Ikechukwu Eze, inda yake mayar da martani ga wani kungiyar siyasa mai suna APC Reformation Forum wanda ta yi zargin Lyon ya baiwa Jonathan miliyan 300 da mota a shirye shiryen rantsar da shi gwamna domin ya kula da bakinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng