Bidiyon Muhammadu Sanusi II a jirgin sama bayan an tunbukesa daga mulki

Bidiyon Muhammadu Sanusi II a jirgin sama bayan an tunbukesa daga mulki

Mun samu wani bakon bidiyo da aka ga tsohon Sarkin Birnin Kano, Muhammadu Sanusi II a cikin jirgin sama bayan an sauke shi.

An dauki wannan bidiyo ne yayin da Malam Muhammadu Sanusi II ya ke cikin jirgi a hanyarsa ta zuwa babban birnin tarayya na Abuja.

Idan ba ku manta ba, bayan an tunbuke Muhammadu Sanusi II daga gadon sarauta, ‘Yan Sanda sun turo jirgi ya dauke shi daga fada.

Jami’an tsaro na ‘Yan Sanda da na hukumar NSCDC su na cikin wannan jirgi tare da tsohon Mai martaban inda su ka yi gajerar tafiya.

Bayan sun tashi da kimanin karfe 6:40 na yamma, Sanusi II ya isa babban filin jirgin sama na Nnmadi Arzikwe ne bayan karfe 7:00.

KU KARANTA: Kwankwaso ya ce akwai hannun Buhari a tsige Sarkin Kano

Ko da tsohon Sarkin ya juya baya yayin da wasu ke daukar wannan bidiyo, za a iya ganinsa da rawani da alkyabbarsa mai launin goro.

Bayan Jami’an tsaro akwai wasu tsirarrun Hadiman tsohon Sarkin da kuma na-kusa da shi cikin Tawagar da ta yi masa rakiya daga Kano.

Bayan sauka a filin jirgin Abuja ne tsohon Sarkin ya tafi Garin Loko cikin dare inda Sarkin Garin ya tarbe sa da kimanin karfe 2:00 na dare.

Bayan shafe kusan sa’a bakwai a hanya, an kuma dauke Muhammadu Sanusi II daga Loko zuwa Garin Awe a Nasarawa idan ba ku manta ba.

Kamar yadda wannan bidiyo da Gidan Talabijin na TVC su ka wallafa ya nuna, babu Iyalin Mai martaban tare da shi a cikin wannan jirgi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel