Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a majalisar dokokin Kano kan tsige Sarki Sanusi

Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a majalisar dokokin Kano kan tsige Sarki Sanusi

Mambobin majalisar dokokin jihar Kano sun barke da fada da safen nan yayinda kwamitin binciken sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ke shirin gabatar da rahoton kwance masa rawani. Daily Nigerian ta ruwaito.

Rikicin ya fara ne yayinda mataimakin kakakin majalisar, Hamisu Chidari, ya nemi izinin gabatar da rahoton yau.

Amma yan majalisar jam'iyyar adawa ta PDP suka ce a dakatad da gabatar da rahoton binciken sai ranar Talata domin kara dubi cikin rahoton; kawai sai rikici ya barke wanda ya kai ga dan majalisa mai wakiltar Warawa ya dauke sandar majalisa.

Masu idanuwan shaida sun bayyana cewa akwai alamun cewa yau za'a kwancewa sarki Sanusi rawani ko ta rahoton majalisar, ko kuma ta hukumar yaki da rashawar jihar.

Ku dakace cikakken rahoton...

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel